Music Video
Music Video
Credits
PERFORMING ARTISTS
Ali Jita
Performer
COMPOSITION & LYRICS
Ali Jita
Songwriter
Lyrics
[Intro]
Saminai, saminai
Saminai, oh saminai
[Verse 1]
Sunanta amarya
Takenta amarya
Yau an ƙure karya
An ɗora tukunya
Sannun ki amarya
ʼYa ce ʼyar manya
Da waya ayi zarya
An saba musaya
Kallon soyayya
Sai kin yi amarya
Ga share gida ma
Kin yi shi amarya
Sai kin yi abinci
Kin ba shi amarya
[Chorus]
Saminai, saminai
Saminayo, saminai
Saminai, saminayye, saminai oh saminai
[Verse 2]
Jita na ɓullo
Ku fito ku yi kallo
Harkar da na ɓullo
Jirgin da na shillo
Ango ya ɓullo
Yau shi aka kallo
Yi wa tuzuru gwalo
Kai ka kasa dolo
Kai ka yi musu zillo
Duk inda ka ɓullo
Ƙauna, ƙauna ce
Har kun ƙure kwallo
Wa zanyi wa gwalo?
Mai ƙin ya yi kallo
[Chorus]
Saminai, saminai
Saminayo, saminai
Saminai, saminayye, saminai oh saminai
[Verse 3]
Soyayya ta yi
Zuciya na sanyi
Kin samu masoyi
Mai ɗauke nauyi
Alƙawari kun yi
Kuma Allah ya yi
Yau babu bulayi
Kuma ba juyayi
Kallon shi kike yi
Kallon ki yake yi
Zancen shi kike yi
Zancenki yake yi
Begenshi kike yi
Begenki yake yi
Kaunar shi kike yi
Ƙaunar ki yake yi
Murmushi kin yi
Shi ma kiga yayi
Ke ce yar yayi
Shi ma dan yayi
Ba shi ruwan sanyi
Zai ba ki na sanyi
Yau Allah ya yi
Auren ku ake yi
Kina kallon sa
Yana kallon ki
Kina mararin sa
Yana mararin ki
Kina maganarsa
Yana maganarki
Ki ce mi shi darling
Ya ce mi ki baby
Kice mi shi sarki
Ya ba ki sarauta
Sannun madubin dubawarsa
Ya ba ki amana
Kin ba shi amana
To mai ya yi saura?
Ni babu ruwana
[Chorus]
Saminai, saminai
Saminayo, saminai
Saminai, saminaye, saminai oh saminai
[Outro]
Saminai
Saminai oh saminai
Saminai, saminai, saminai
Saminai, saminai, saminai
Saminai, saminai
Saminai, saminaye
Saminai, oh saminai
Saminai, saminai, saminai
Saminai, oh saminai
Saminai, saminai, saminai
Saminai, oh saminai
Saminai, saminai, saminai
Saminai, saminai, saminai
S-s-sultan with the beat baby
Written by: Ali Isah Jita


