Music Video

Music Video

Lyrics

Salamu alaikum
Sallamar Musulunci mukayi masoya
Abokina ya rayuwa?
Ya aka sha fama da dawainiya?
Yasu umma yasu abba?
Ya ankai fama da masoya
Ina magana ammah gani nake fuskar ka da damuwa
Fada mini menene don zuciyata kar tayi tsarguwa
Zaman da mukai na jiya mun rabu nasan baka da damuwa
Ka tuna mini labarin masoyiya mai sanya hawaye
Ummi jiya tace min batu na auren nan an janye
Kuma bayan mun shirya ina tunanin tura iyaye
Ni ina tsoron kodai zuga take dauka ta kawaye
A'ah ni a zaton da nake da kanta tayi canjin halaye
Kale komai kaddara ce in ya nufa sai anyi a raye
Kaga ni da Nafisa sai da nayi kaman in kaita kiranye
Gata bata yawan magana, shiru-shiru halin sufaye
Haba ai nasanta Nafisa bata biye hali na kawaye
Wai menene matsalar? Ka duba can ma yadda ya faru
Kai da Aisha kun bata na gwada sulhun yaki ya gyaru
Laifin daga matan ne ina gudun ni kar in kwaru
A'ah ko daga gun ka yake aboki ko sai dai mun taru?
A'ah kai kasan komai aboki kasan bani da daru
Na tuno da Amina yar Yola wacce tayi zama a Kaduna
Yar Fulani fara kyakkyawa wacce bata fadin suna na
Aboki tuna ka gani rumi-rumi ma kayo bankwana
Gashi dai mun shaku da juna muyi ta waya a dare ko rana
A gidan su da yara da manya kowa na ta fadin suna na
Kwatsam sai ga sako a cikin waya an sa mata rana
Har na tuna Hauwa'u maijidda mai kyau yar Katsinawa
Tana matukar sona a kaina ma bata kula kowa
Bata tafiya makaranta sai na biya mata in takawa
Ammah daga karshen-karshen an mata aure tayi tarewa
Noma tushen al'ada, garin Jigawa nayi budurwa
Halima kake zance, Allah sarki yar talakawa
Tana da yawan ilimi, a jarabawa ta wuce kowa
Itama daga karshen zance na rasa yadda mukayi rabewa
Wai ina Hajara ta Minna? Bata da kyan fuska sai baiwa
Kace mini yar boko, mai son halayen turawa
Itama haka mun kaiyo, saida mukayi suna gun kowa
Ashe ita burin ta a Ingila taka san zaunawa
Sai Shuwa kuma sai larabci yan matan Maiduguri
Ga ado kuma ga gashi, su matsalan su rashin hakuri
Har na tuna zahra fara, yar Maiduguri
A zaton da mukayi soyayyar da munkayo tayi min sihiri
Daga karshe an mata aure ni kuma na fada garari
A Yobe ina da budurwa ni bansan mai nayi mata ba
Nace zan kai kaya yayan ta yace ba haka ba
Kuma na shawarce ta, tace a sa manya a gaba
Tuni sun mata auren dole ai basu ma kyauta mata ba
Mai masa yar Bauchi na gaza in mata ma uzuri
Kace Maryam kenan mai sawa masa sukari
Ita wai sharadin auren, bata son waje sai na gari
Wayyo Allah Ladidi, Ladidi yar lele yar baba
Ya garin Birnin Kebbi kenan mai jita in ban manta ba
Ta soni kamar gaske, ashe ubanta yana wani duba
Mun je Birnin Shehu, ran nan a Sokoto mu sauka
Barira ce ta bamu ruwa, mun gode maku har Baraka
Ai abin daga Allah ne, a haifa dan kura da jaka
Kanon dabo babban birni garin mu mai mota mai mata
Garin Naira da Kobo, garin mu mai babbar masarauta
Garin Sarkin Kano, sarki mai halin kyauta
A Abuja mun sauka, muka so muji kunya
Garin su Halimatu birni nan ne mahaifar su Sa'adiya
Aboki kabar zancen nan don Allah bansan tuna baya
Halin mata da yawa, daban-daban wasu sun cika karya
Written by: Ali Isah Jita
instagramSharePathic_arrow_out

Loading...