Crédits

INTERPRÉTATION
Ali Jita
Ali Jita
Interprète
COMPOSITION ET PAROLES
Ali Jita
Ali Jita
Paroles/Composition

Paroles

[Verse 1]
Ai wannan kiɗan da daɗi
Ba wanda na yiwa sai Rahama
Na doka tambura na
Ga jita tana ƙiran Rahama
Kowa yazo yaji ba laifi kuna da wani Rahama
Girma yana da rana lalle ranar shi kin gani Rahama
Ataka a hankali ga zarewa tana faɗin Rahama
[Verse 2]
Sannunki Gimbiya, sannun ki adala Rahama
Sannunki jaruma, kuma sannun ki malama Rahama
Sannunki Hajiya, mai ɗan abin biki Rahama
Mata suna faɗa, baiwa kinfisu Gimbiya Rahama
[Verse 3]
Mai kyau da ƙwarjini, ga haƙuri gurin Rahama
Girmanki naki ne, waye yake gudun Rahama
Ki ƙyale mahassada
Kinga kinsamu ɗaukaka Rahama
Aboka da maƙiya wannan dai lokacinta ne Rahama
[Verse 4]
Jirgi yazo gari, bakomai zaiba zaya ɗau Rahama
Ga ʼyar sarakuna, Rahama sannan ɗiya ta malumma
Giwa nace dake, kin ɗara mata dubu dubu Rahama
Mata adon gari, bawani birni da babuke Rahama
[Verse 5]
Tauraruwar gari, haske da walƙiya Rahama
Kwarkwasa nada haushin kifi, shi kuwa yana ruwa Rahama
Boka yana da haushin Malam, Malam yana da alfarma
Tafiyan gari da nisa wanan lallai a barwa raƙumma
Ke addu'a ashe tuntuni an amsa addua'r Rahama
[Verse 6]
To ga ƙiran da nayi shima zai amsu gunki ke Rahama
Sallah kina tayi, ki ƙara da nafula Rahama
Sannan wajen shiga, hijabin ya rufe jiki Rahama
Kowa ki gaidashi girmanki nakine Rahama
Ramattu Gimbiya, koko muce dake Rahama
[Verse 7]
Aljanna nada suna amman sunanta ma gidan Rahama
Ramattu Gimbiya, koko muce dake Rahama
Ki taka ki rausaya kinji wannan kiɗankine Rahama
Ali jita ya gaida ke, don kyan halinki ne Rahama
Written by: Ali Isah Jita
instagramSharePathic_arrow_out

Loading...