क्रेडिट्स

COMPOSITION & LYRICS
Ali Dan Saraki
Ali Dan Saraki
Songwriter

गाने

لَا إِلٰهَ إِلَّا ٱلله
Ba gwani sai Allah
Allah ka taimaki soja
To ko gidan mu koda daji
Ko a bakin daga
To ko gidan mu ko gun yaki
Amma banda aikin soja
Wa za'i kwana a rami?
Ya kwan a gindin dutse
Wallahi ga ruwa na duka
Amma saboda neman yanci
Akuya ta cire wa kura bindi
Ta sha aradu sai ta rama
Dan mutuwa yan maza suke guje soja
Ko gida tana kashe kato
Dan bata tausayin dan yaro
Amma na fadawa 'ya'yan soja
Zanyi tambaya a gareku
A filin daga, idan wuta tayi wuta
In wuri yayi wuri
Soja ba'a ce muku Allah
Sai kun kashe mutum zaku san shi
Amma nasani a filin daga
Idan guri yayi guri
Idan wuta tayi wuta
In an rasa hanya
Idan waje ya tude
Sai an hada da yan adilare
Maza manema suna
Na gomna yanyamawan daji
Bayan wuta ina wani aikin?
Ina maza manema suna
Lokacin ana bude wuta
Wuri yayi wuri
Wadan sojojin mu
Sun haura ruwa
Wadansu na nan gefe
Naji tausayin wani soja
Ga gada ta karye
Naji tausayin wani soja
Su baba tsufa yazo
Ga zuciya tana son yaki
Maza manema suna
Na gomna yanyamawan daji
Bayan wuta ina wani aikin?
Akuya ta cire wa kura bindi
Ta sha aradu sai ta rama
Amma na fadawa 'ya'yan soja
Saboda ikon Allah
Ku sani a soja
In kuka sani a soja
Inje training depot
Idan na kare training
Ku bani rigar soja
Ku bani wandon soja
Ku bani takalmin ku
Bindiga ku harba abin ku
Kuna wuta ina muku waka
Written by: Adamu Dan Maraya Jos
instagramSharePathic_arrow_out

Loading...