Adbull D의 상위 곡
유사한 곡
크레딧
실연 아티스트
Adbull D
실연자
Umar M Sharif
실연자
작곡 및 작사
Adbull D
작곡가
abdulkadir tajuddeen
송라이터
가사
Abinda yake raina zana fitar in huce takaici
Soyayya ke damu na zana fada bazan boye ba
Nima abinda yake raina zana fitar in huce takaici
Soyayyar ki a raina zana aje ba zata fice ba
Hmmm, alamar tambaya tana ga mai yawaita tunani
Musamman in ya shiga halin soyayyar zamani
Yau gani cikin ta na rasa wanda zai fidda ni
Sai kai masoyina wanda muka yi kyau da kamanni
So a aikace, fayyace, yafi dace
Ni a mutumce, kai zance ban canzawa
Na gamsu da surarki, tsarinki har kyawunki
Nima ina sonki, kwatankwacin kalaman baki
Kallon so ya tsuma ni har nayi ra'ayin kaunar ki
Ni dake in muna tare, babu mai raina ki
Na rike kauna tarayya ta zauna
Nayi shiri na zan kare dukka hakkin ki
Rawa da girgiza zanyi gabanka in jujjuya
Zanyi maka albishir kayi dace da mai tarbiyya
Sannan zan zame maka farin ciki na nan gidan duniya
Nafi kowa saninka cikin abinci kafi son taliya
Zanyi rubutu, karanta ka fahimtu
Na ilmintu a sonka nayi morewa
Ko a kwatance banda yake nayi godiya
Na kara hasashe, babu yake gun kwalliya
Zabi na kece da gani babu tambaya
Dawisu gurin ado babu yake kyan duniya
Taho mu zauna
In baki kauna
Taho ki rike
Masoyiya
Lyrics powered by www.musixmatch.com