Teledysk

Teledysk

Tekst Utworu

[Chorus]
Babbar yarinya nayi sa'a
Na zamo auta cikin maza
[Chorus]
Haɗuwar mu da kai shine sa'a
Bayani dace a ʼyan mata
[Verse 1]
Hankali ke sa ayo girma
Natsuwa mataki cikin girma
A gurin ki dukkan su kin sama
Ko a cikin sunanki akwai girma
Babbar yarinya laƙabin ki
Ke na raɓa don nayo girma
[Verse 2]
Duhu mai dusashe haske
Dukkan mai ido shi zaya faɗan ma
Idan akwai ka ba'a batu na
Ganin mu da kai ke ƙaran girma
Manyan yara da sun ganka
Su zo da sauri kai su karrama
[Verse 3]
Ni so da ƙauna shi nake nema
Indai a guna ne tuni ka sama
Lallai gare ki ina da alfarma
Ko wani ka kawo ka sani zanyi ma
So yakai so tsakanin mu
Bana gajiya gun yi miki hidima
[Chorus]
Haɗuwar mu da kai shine sa'a
Bayani dace a ʼyan mata
[Chorus]
Haɗuwar mu da kai shine sa'a
Bayanin dace a ʼyan mata
[Verse 4]
Nazari nayo a kanki
Da tabbacin banyin nadama
Kinyi min shimfiɗa ta fuska
Zahiri ta zarce tabarma
Nayi rawa a gaban ki na taka
Zo kimin naki sallon kema
Allah nunan masoyan mu
Ka tsare mu sharri na ʼyan gulma
[Verse 5]
Kayo nisa cikin raina
Ba'a hangen ka bare a cimma
Ganganci ne a ce za a iske ka
Ko dan gajiyar tafiya a tsuma
Tunda na tsinke zaren burki
ʼYan samari sai kuyi ta himma
[Chorus]
Babbar yarinya nayi sa'a
Na zamo auta cikin maza
Haɗuwar mu da kai shine sa'a
Written by: Umar M Shareef
instagramSharePathic_arrow_out

Loading...