album cover
Shafa'atu
32
Afro-Beat
Shafa'atu was released on April 30, 2018 by Apple Media Africa as a part of the album Iconic Sounds of Africa Vol, 69
album cover
Release DateApril 30, 2018
LabelApple Media Africa
Melodicness
Acousticness
Valence
Danceability
Energy
BPM95

Lyrics

Zo Shafa'atu kyakkyawa
Yar dangi mai kyawon asali
Garin so bai nisa dawo na gan ki abar so na
Na dade a maraicin soyayya ki amsa kalamai na
Kai nake ra'ayi kullum zancen ka shine zance na
Son ka ya zama hoto a zuciya madubin duba na
Kai na bai wa amana yau kullum da son ka nake kwana
Mai abin so ya huta na samu wacce nake nema
Kai kazam mini alkibla ka taho kayi mini alfarma
Banda 'ya tamkar ki a soyayya dake zan fahari ma
Zuciya ta wanke ga ajiya tana faman nema
Hankali ya karkata gun ki gamo dake shi nayi nema
Ai garin so bai nisa yau gani gun ka masoyi na
Zo Shafa'atu kyakkyawa
Yar dangi mai kyawon asali
Garin so bai nisa dawo na gan ki abar so na
Na dade a maraicin soyayya ki amsa kalamai na
Bani ji da jiyarwa yanzu batun kane fah karatu na
Yau batun Adabin soyayya taki ce a rubutu na
Kwanciya, tashi da zama bana rabo da masoyi na
Kin zamo tauraron haskaka zuciyata mai sona
Alkawar na dauka a son ka ba dare kuma ba rana
Zahiri soyayya ta gaskiya muke yiwa juna
Kai nake ra'ayi kullum zancen ka shine zance na
Son ka ya zama hoto a zuciya madubin duba na
Kai na bai wa amana yau kullum da son ka nake kwana
Yanzu na rike soyayya
Da gaskiya na dau niyya
Zo taho mai alkunya
Gare ki nayo dubayya
Son ka nima na dauka
Nayi nutso kogin son ka
Zo kayi mini son barka
In zamo mata gun ka
Kai nake ra'ayi kullum zancen ka shine zance na
Son ka ya zama hoto a zuciya madubin duba na
Kai na bai wa amana yau kullum da son ka nake kwana
Yau na samu diya ta mutunci yar gidan alfarma
Sahibi kyakkyawa kai na rika na saka a dama
Tarbiyyar ki da halin kirki su nake duba ma
Gaka mai ilimin addini kai nake ra'ayi ma
Kin zamo mai kyautata sallah ga yawan azumi ma
Mai riko da salatin annabi kai na bai wa batu na
Tushen alkhairi farko na samo daga ummi na
Sun sani akan hanyar Islama ne addini na
Sallah da salatin annabi shi na rike ga ma'aiki na
Written by: Hussaini Danko
instagramSharePathic_arrow_out􀆄 copy􀐅􀋲

Loading...