Music Video

Music Video

Credits

PERFORMING ARTISTS
Umar M Sharif
Umar M Sharif
Performer
COMPOSITION & LYRICS
Umar M Sharif
Umar M Sharif
Composer

Lyrics

Kun gani, kun gani riga ra'ayi ce
Ra'ayi riga na sanya ka
Ra'ayi riga
Zabi na gata
Kun gani, kun gani
Ra'ayi riga
Zabi na ga shi
Kun gani, kun gani
Tunda kin bani so, ni kuma, ni kuma na baki kauna
Nayi miki guri, zo a cikin zuciyata ki zauna
Rayuwata dake zata fi dadi farin ciki na
Ba muyi yin fada tunda mun san hali na juna
Bani jin rada kan ki kece zabi na rai na
Zo muje mu huta ni dake a lambu na kauna
Zabi na, gata
Kun gani, kun gani
Kari na so shine ya harbe ni a jiki na da dafi
Ya saka ni maye da alamu ya karya kafi
Farin ciki ya kawo bakin ciki ko ya tafi
Ya saka ni daki mai kyau da an kayi wa rufi
Ga sanyi babu zafi
Yana ta ban kula ko idanuwa sun nuna
Shi sirri anfi so kar da a bayyana
Ga wanda anka bai wa sai ya adana
Ba nuna gajiya ne ba ka rissuna
Ga wanda ka kafi in dai zaka amfana
Komai kika sanya ni sai nayi in dai da so da kauna
Na zama bawan ki aiki na ne shi ya nuna
Shi waiwaye ado ne ga matafiyi
Riga kowa akwai tashi ta ra'ayi
Ni kun ga nawa zabin dan saurayi
Fari na gan shi ko ya wuce gawayi
Autan maza na yayi
Kaunar ka shi nake yi a zuciya ka zauna
Ra'ayi riga
Zabi na gata
Kun gani, kun gani
Kun gani, kun gani riga ra'ayi ce
Ra'ayi riga na sanya ka
Ra'ayi riga
Zabi na gata
Kun gani, kun gani
Ra'ayi riga
Zabi na ga shi
Kun gani, kun gani
Written by: Umar M Sharif
instagramSharePathic_arrow_out

Loading...