album cover
Siyan Baki
1,761
World
Siyan Baki was released on May 3, 2018 by Apple Media Africa as a part of the album Iconic Sounds of Africa, Vol. 7
album cover
Release DateMay 3, 2018
LabelApple Media Africa
LanguageEnglish
Melodicness
Acousticness
Valence
Danceability
Energy

Music Video

Music Video

Credits

PERFORMING ARTISTS
Nura M. Inuwa
Nura M. Inuwa
Performer
COMPOSITION & LYRICS
Nura Musa Inuwa
Nura Musa Inuwa
Lyrics, Composer

Lyrics

Eh, amarya gaishe ki
Kice ragamar daki
Lamuran ki da mamaki
Ga ragama kin zamo ki daure maza
Siyan baki dai sai ruko kaza
Kamar ranar sallah
Idan kun ga shigar ta? amarya (sha'aninki)
Ashe ranar wanka ko da an rufe cibi bashi boya (sha'aninki)
Da zarar an kai ki kowa zaya tabaki yayi karya (sha'aninki)
A kan ki nake kishi
A kan ki ake bashi gaya (sha'aninki)
Zo ki karbi kudin tushe
An biya maki ba bashi
Ya ne naga hannun kamar musaya (sha'aninki)
Idan an hana koh daya ku jaya (sha'aninki)
Da zaki kuna bata kai magarya (sha'aninki)
Kinji zaki shige lalle
Yau kafa taki an kulle
Sadaki ne ka sayi (sha'aninki)
A kan hanya akan tsanki zarya (sha'aninki)
An biyo ki ana guda
Mai gida ya siyo kibga
Mai lissafi bai gurin hidaya
Farar aniya sai ta zama laya (sha'aninki)
Naji bakya yin laifi
Inji masu gurin girki
Cikin magana toh mu daina karya (sha'aninki)
Mu gyara zukata mu kyauta niyya (sha'aninki)
Sai mu dinga gudan harshe
Kar dukkan mu rurushe
Kauna ta ce maganin kiyayayya (sha'aninki)
Dukkan rai ba na ga biyayya (sha'aninki)
Kar ki zarfafa yin kishi
Ko da sukar harsashi
Rikon baki ne su bada zarya (sha'aninki)
Akwai banbanci gun gyare da zanya (sha'aninki)
Dau wukar ki, ki dan wasa
Dan wasun koh akwai kisa
Su ka dan yi fari ido su juya (sha'aninki)
Domin sunyi fice su barki gaya
Hikimar ki, ki sarsarka
Tada kan ki ki dan leka
Abunda suka zo da shi ki koya
Garin dai koh wangale wushirya (sha'aninki)
Ja zaren ki kiyo tubka
Kar kije ga sarar suka
Na sanya ki a san sanin masoya (sha'aninki)
Yan bori sun fi son kidan garaya
In da rana akwai sata
Daudawa ma da warin ta
Mallacci shi ake tsumayaa (sha'aninki)
Mai barci shi zaya sa karaya
Furuci na bulale
Kan wacece zan sola?
Ballagaza ita na gano a kurya (sha'aninki)
Da sakarci ta rike ta kwarya (sha'aninki)
Kwan, kwan anyi bugun kofa
An baya rumfa
Ashe baki aka zo siyayya (sha'aninki)
Tukuicin a yau rago na layya (sha'aninki)
An nishe ki cikin tuffa
Ga mayafi kin yafa
Zance na shi ne ki dai na kunya (sha'aninki)
Amarya na san kina da kwanya
Magana kiyi wa ango
Ki ga dai shi ne jigo
Sai ya kawo za a sa tukunya (sha'aninki)
Abokai dukka sun ka yo kamarya (sha'aninki)
Ango naki akwai tsafta
Naga yayi shigar kufta
Domin kauna ne yake kwaranya (sha'aninki)
Allah damu da rai gari mu waya (sha'aninki)
Wani takun kasaita
Sai amarya an kai ta
Nan zaki ji sallo na kashe murya (sha'aninki)
A nan aiki ma sai anyi kuya (sha'aninki)
Ga nasiha ta gun ki
Kin yaban ya satoki
Ki dau bangoro sai ki kyale danya (sha'aninki)
Man shanu ya zarce man kadanya (sha'aninki)
Nura ne ke yin waka
Masu cizo su sa kika
Kunama ke bibiyar ki ginya
Fulani ka muamala da kwarya
Written by: Nura Musa Inuwa
instagramSharePathic_arrow_out􀆄 copy􀐅􀋲

Loading...