Credits

PERFORMING ARTISTS
Arewa Sound
Arewa Sound
Performer
COMPOSITION & LYRICS
Nura M. Inuwa
Nura M. Inuwa
Songwriter

Lyrics

Ehh, rana dubu ta soyayya
Nai tsintuwa akan hanya
Ku shigo gidan cikin tsari
Da dukanku zanyi tarayya
Rana dubu ta soyayya
Munyi tsintuwa akan hanya
Wanda ya zamo cikon buri
Shi akaso a tarayya
Murna dake ina shauki nai tsintuwa (masoyina)
Dake zana bare soyayyata sabuwa (ina murna)
Kuma zan dagaki in daura kololuwa
Lale da kai masoyina mai ra'ayi daya (ina sanki)
Samun kane cikar burina rike gaskiya (bani barin ki)
Ko bangaren hadin kai samun dare tsintsiya (hmm)
Dauke ni muje gida (masoyi)
Hanya marar gargada (masoyi)
Ba mai mana ka'idaaaa
Soyayyace ta gamon jini
Bakai yazanyi na rayu ni?
Yau mun gamo zama nan gani
A soyayya
Rana dubu ta soyayya
Munyi tsintuwa akan hanya
Wanda ya zamo cikon buri
Shi akaso a tarayya
Saqa ta saqa alkairi
Kaikai yatai gamai shika
Daga zuciya nake furta maka gaskiya ina sanka
Gonarka na bukatar samun ban ruwa jikin shuka
Eh, farin ciki ya cika raina
So na hada miki da kauna
Na bude sirri na ciki na
Nagane kin gane nufi na
Nabar miki kaina
Fansar ki rike rana dubu ta tarayya
Eh, rana dubu ce ta tabbatar wa da rai ina sanki, ki gane
Komai rabo ne dani dake so baza mu ware ba, hakika
Rana dubu ce ta tabbatar wa da rai ina sanka, ka gane
Komai rabo ne dani dakai so baza mu ware ba, hakika
So wani ciwo ne
Da yakkajin kunne
Ance makaho ne
Dafinsa mugu ne
Yasani nai zaune
Eh, ki soni in soki
Ina tinanin ki
Irin kalaman ki
Akan su komai zana mika
Rana dubu ce ta tabbatar wa da rai ina sanka, ka gane
Komai rabo ne dani dakai so baza mu ware ba, hakika
Kin bani na amsa
Na soki ba wasa
Koda fagen gasa
Kowa da zabin sa
Ke kinfi kwarkwasa
Mu shuka alkairi
Hadin mu mai tsari
Na wuce yin gori
Duk inda kai ni zana bi ka
Eh, zo mai sona
Kin zama linzami guna
Kibiyar kaunarkice tasoke min raina
Ke na zaba
Ki aminta miyi zaman tare
Zo mai sona
Ka zama linzami guna
Kibiyar kaunarka ce tasoke min raina
Kai na zaba
Na aminta miyi zaman tare
Ina da labari gunki
Adonki yayi da jan baki
Ai dole nai miki kakaki
Ganinki na dada gan doki
Me zan da wata idan gaki?
Daga ni sai kai soyayyar mu akwai dadi
A rake zaki ba'a gayawa gyda gardi
Sama tai nisa yan kasa ke takun fadi
Idan nazo masu kulaka subar kaudi
Ka fada musu nai kere
Da kalaman so kika sace tinanina
Daga bege sai na tsananta cikin kewa
Da kalaman sonka ka sace tinanina
Daga bege sai na tsananta cikin kewa
Duniyar so mu yakamata mu rayu ciki
Ayi taro ran shagali namu ayi biki
Na rikeka idan ka guje ni ka dauki haki
(Na amince) kayi abinda nake fata
(Mu kasance) muy tazara acikin mata
(Sama zarce) yadda wadansu suke cewa
Yanayinka kamanina
Da kalaman so kika sace tinanina
Daga bege sai na tsananta cikin kewa
Ga idona yaga abinda yaso kallo
Fitila ta ke nagani a cikin falo
Zama zarani wata ta sama na bullo
(Kayi zane) ina na fada ki karanta min
(Da mutane) dan gyda kai ki kwatanta min
(Maganar so) ita a sirri ake yinta
Ke fadeta a kunne na
Da kalaman sonka ka sace tinanina
Daga bege sai na tsananta cikin kewa
Ka yarda na yarda nima rana dubu cikin rayuwata
Farin cikina tazo mukai maganin dukan damuwata
Ba matsala agurina mudin ka yarda zamuyi aure
Kina da kyan halaya
Domin ko baki hamaya
Ke zana ba soyayya
Farar diya mai kunya
Ni ke nake kauna
Na zama nice ta farko
Rikon kayi mun na karko
Turo ayi mana baiko
Akanka ni nayi sakko
Na kara himma na tako
Ga dan furena na tsinko
Na baka kyawun gani na
Written by: Nura M. Inuwa
instagramSharePathic_arrow_out

Loading...