Lyrics
[Verse 1]
Soyayya ruwan zuma ce, yara kusha ku bai masoyi
Yau da gobe na ga Allah don haka duniya tabawa
[Verse 2]
Soyayya ruwan zumace, yara kusha ku bai masoyi
Yau da gobe na ga Allah don haka duniya tabawa
[Verse 3]
Eh! Soyayya ruwan zuma wasu ko suka ce ruwan gubace
Wasu ta daga su amma ga wasu ta aje su kwance
Wasu sunyi arziki sanadi nata wassu na ta rance
Wasu sammako suke mata wasu su yo fitar maraice
Wasu ma gudu suke yi tunda shigarta matsalace
To a kan ta ya ake ne gata jikin yaro da babba
[Verse 4]
Soyayya ruwan zumace, yara ku sha ku bai masoyi
Yau da gobe na ga Allah don haka duniya tabawa
[Verse 5]
Eh! wasusun riketa sosai soyayya ai ni'ima ce
Ita ke batar da laifi wanda a kai wa ya makance
Wasu sun yi nasara wasu ko a gurinsu kaddara ce
Wasu riba suka irga wasu asara suka yi zance
Haka bai sa su kasa komawa so baya suka mance
Wanda zayyi ban hanashi don gargadi ba zai jiyaba
[Verse 6]
Soyayya ruwan zuma ce, yara ku sha ku bai masoyi
Yau da gobe na ga Allah don haka duniya tabawa
[Verse 7]
Eh! haka daidai fadi tashi irin tafiyarmu ta kasance
Yanayi irin na cutar soyayya ba ta jin surace
Ita ke raba mutum da mutane yai ta son kadaice
Yai ta zaro magana a rashi na sani don ya dimauce
Uzuri za na yi mai shi ne daidai ko a hukunce
Wanda dukka ya yi nisa kun ga kira ba zai jiya ba
[Verse 8]
Soyayya ruwan zuma ce, yara ku sha ku bai masoyi
Yau da gobe na ga Allah don haka duniya tabawa
[Verse 9]
Soyayya ruwan zuma ce, yara ku sha ku bai masoyi
Yau da gobe na ga Allah don haka duniya tabawa
[Verse 10]
Gangar jikinka ba ta aiki in zuciyarka na a sace
Ita kibiya ta soyayya ba. ayi mata kuace-kauce
Don kamar jini d ahnata ne tabbacin ko akwai kawance
Soyayya ba a ganinta bare ai zaton wacce siface
Launi ko da kala ta gagara masu tance-tance
Ga rubutu bisa allo marar ido ba zai biya ba
[Verse 11]
Soyayya ruwan zuma ce, yara ku sha ku bai masoyi
Yau da gobe na ga Allah don haka duniya tabawa
[Verse 12]
Ko da hannu ba a rikonta bare ka damke ta a yi kwace
Ita soyayya ba ta tsufa bare a ce tana da kwance
Ba ta jin zuga saboda irin lamari na masu bace
Ga shi ba taguwa bace bare ka sanya a ce ka since
Wanda yai zurfi a cikinta sai ta sa shi ma ya zauce
A tsaye kamar mutum ne kai magana ba zai sani ba
[Verse 13]
Soyayya ruwan zuma ce, yara ku sha ku bai masoyi
Yau da gobe na ga Allah don haka duniya tabawa
[Verse 14]
Babu yadda za mu yi wa soyayya kun ji zan takaice
Ta biyo cikin jini na waiwayi baya salsala ce
Ka gani ka ce kana so in aka so sai a amince
Sanadin wannan abar soyayya wasu sun talauce
Wasu na san za su ja da hakan su fada wai kirkira ce
Nazari don fahimta in kuka ja ba zan hana ba
[Verse 15]
Soyayya ruwan zuma ce, yara ku sha ku bai masoyi
Yau da gobe na ga Allah don haka duniya tabawa
[Verse 16]
Soyayya ruwan zuma ce, yara ku sha ku bai masoyi
Yau da gobe na ga Allah don haka duniya tabawa
[Verse 17]
Soyayya ruwan zuma ce, yara ku sha ku bai masoyi
Yau da gobe na ga Allah don haka duniya tabawa
Written by: Farouk M Inuwa, Isa Gombe, Mubarak Dutse, RR