album cover
Zaurance
89
Afro-Beat
Zaurance was released on April 30, 2018 by Apple Media Africa as a part of the album Iconic Sounds of Africa Vol, 69
album cover
Release DateApril 30, 2018
LabelApple Media Africa
Melodicness
Acousticness
Valence
Danceability
Energy
BPM129

Credits

PERFORMING ARTISTS
Hussaini Danko
Hussaini Danko
Performer
COMPOSITION & LYRICS
Hussaini Danko
Hussaini Danko
Composer

Lyrics

Zaurance a Hausar magana fira ce
Da kwatance ake bai wa zukata wuri
Zaurance a Hausar magana fira ce
Da kwatance ake bai wa zukata wuri
Salon mu da tafa-tafa so na bar miki yanmata
Sanar mini in kin karba in ga na hada yarda ta
Dake naga yayi dacewa inga na hada jinga ta
Ki yarda ki lamunta
Kizam mini mata ta
Muyi rayuwa
Mu ga shakuwa
Idan na taho, kin taho, su taho gare ni fuskanta
Suna dauke algaita
Na busa ga mai tsafta
Ke zaki zami mini yar shagwaba zaman ki gida na
Na lura dake komai kika so nai miki na dau alkawari
Zaurance a Hausar magana fira ce
Da kwatance ake bai wa zukata wuri
Tsaya kaji babban zance kar nasa ka a kokwanto
Da zuciya ta lamunce dole za'a ga daidaito
Sanar maka na tantance sirrika duka zan kwanto
Na kai maka karshen zance kai ka zam mini sha zanto
Na gamsu ni
Ka rike ni ni
Kai nake gani
Da tuna-tuni
Mai son ya raba zai ja rigima da bata da rana
Jini na jiki ya kamu da so da gaske da kai zan alfahari
Zaurance a Hausar magana fira ce
Da kwatance ake bai wa zukata wuri
Yau harshe fadi soyayya, kunne saurare
Saurare, na jere, a zaure, gamu tare, turare (turare, turare)
(Turare, turare)
Ki tsaya, na biya miki darusa rike mini
Tafiya, gajiya, ko daya bata zo mini
Aniya, ki iya zaki ki kyautata mini
Ni nayi sabo, da kai nayi yarda
In kaga zanbo, zanen ta ka shaida
In kaji zambo, nan ka mai yarda
Duk yarda ka debo, kauna tayi tsada
Dole cikin maza da kai zan hada hanzari
Zaurance a Hausar magana fira ce
Da kwatance ake bai wa zukata wuri
Kinyi ina gani, zan baki kulawa
Koda ga sansani, kin kayi fitowa
Masu idon gani, ke zasu yabawa
Amsa kiran wani, toh kar ki iyawa
Inda kace na zo, nan zana tsayawa
Tunda a zuciya, kai daya na ajewa
Nayi maka gun zama, don bani cirewa
Kar kayi tagumi, da gaske nayi ma wuri
Zaurance a Hausar magana fira ce
Da kwatance ake bai wa zukata wuri
Zaurance a Hausar magana fira ce
Da kwatance ake bai wa zukata wuri
Written by: Hussaini Danko
instagramSharePathic_arrow_out􀆄 copy􀐅􀋲

Loading...