音乐视频

音乐视频

歌词

Kuji bana so, bana son
Kalmar rabuwa
Kuji bana so, bana son
Kalmar rabuwa
Bana son kalmar nan da anka ce, "Rabuwa"
In na tuno haduwa ta dake ran farko
Da safiyar ranar Juma'a cikin mako
Ina tsaye sai ga kafar ki ta sabko
Cikin wata mota mai kyan gani da aka tuko
Ina ta daukin naga fuskar ki ta leko
Sai sake-sake nake a zuciya koh zan canko
Ashe-ashe
Ashe-ashe
Ashe-ashe
Kama take da turawa
Ashe-ashe
Kama take da Indiawa
Ashe-ashe
Kama take da Larabawa
Banaso so, banaso
Banaso so-so, banaso
Bana son kalmar nan da anka ce, "Rabuwa"
Tunda soyayya ta dake akwai dadi
A lokacin ina tsaye gurin sana'a ta
Sai ta iso tace dani, "In wanke motar ta"
Zata shige salon dan ta gyara gashin ta
Ta bani makuli take sai na fara aikin ta
Kan ta fito har nagama
Ta ban kudi na sallama
Ta ce dani, "Sai anjima"
Gida ta tafi
Bayan ta tafi
Ashe ta yarda passport dinta
Na dauka, na bita da gudu ina so in bata
Na kasa in cin mata tunda tana kan mota
Na bude ciki da na duba akwai adereshi nata
Da na iso kofar gidan na ce, "A kirawo Binta"
Ba tambaya tazo gareni ta fita ba kasaita
Da muka gaisa har na dauko passport dinta na bata
Sai tayi murna
Ta ce, "Tana zuwa in jira ta"
Ko da ta dawo ta bani kudi
Na ce, "A'a Binta"
Nan ta tsaya tana ta kallo na ina tafiya ta
Washe gari Binta tazo ta tarda ni gun aiki
Ta ce dani, "In zo"
Zatan dani ta ce, "Ga wanki"
Sai naji ta furta kalamin so kamar a mafarki
Sai ta juya ta tafi ta barni ina mamaki
Mun fara soyayya dani da ita kamar wasa
Kullum ta dauke ni ta kai ni can gurin wasa
Bacci yake raba ni da ita munyi nisa
Munzama hanta da jini abin kamar wasa
An ce da ita aure sai tace dasu gani
Babanta ya ce, "A bar batun ta kyale ni"
Ba muyi kama ba
Ba mu dace ba a zamani
Abinda ya dace dani da ita shi ne rabuwa
Bana son kalmar nan da anka ce, "Rabuwa"
Tunda soyayya ta dake akwai dadi
Written by: Umar M Shareef
instagramSharePathic_arrow_out

Loading...