歌词
Bangata ba
Amarya ina kike?
Ina kike?
Ga angon ki
Mai kaunar ki
Mai kishin ki
Ya biya sadakin ki
Domin auren ki
Yau dai ya zam naki
Mai kare hakkin ki
Ke kuma ina naki
Menene aikin ki?
Da zaki yi wo angon ki
Ya kara mai sauki
Biyayya shi zakiyi
Da tsafta a dakin ki
Komai in ya sa ki
Kar ki bata ran ki
Balle ki mai tsaki
Ki sani aljanna zaki
Indai kin bi iyayyen ki
Sannan kuma kin bi mijin ki
Toh shine ribar ki
Amarya
Hakuri ribar aure ku dinga duba
Shi zaman tare
Wataran za a saba
Ina kiran ku
Dan Allah banda gaba
Dole watarana muzama Umma da Abba
Fatan da nake mutuwa ita zata raba
Zaman ku ya yo karku abadan abada
Ka rike girma ango Allah ne ya fada
Ke kuma amarya kar kiji su masu rada
Kar ku biye shaidanu burin su ne su hada
Ku rike addu'a ita zata zam magana
Zata zam magana
Zata zam magana
Nagode Allah da ganin wannan rana
Aure na an dora
Na yau rina
Godiya na mika dangi da abokai na
Sannan nai gaisuwa ga dukka masoya na
Dani da amaryata bamu manta wannan rana
Godiya Allah na
Na rasa ta ya zan nuna farincikin ra'ayi na
Komai zance ai kunji shi kurum ango na
Allah kara zumunci yan baya ilahu ya nuna
Allah sa kowa ya koma gida lumi da limana
Godiya dangi na
Dangin ango na
Dada ga ango na
Dada ga ango na
Written by: Umar M Shareef


