歌词
Eyy ni 'yar gata Zaitun, ni 'yar lelen baba
Na gode so kauna, wanda kake nuna min
'Yar gata na Zaitun, sannu 'yar lelen baba
Zo gefena zauna, ban sonki da yin kwalla
Ni sunana Zaitun kuma 'yar baba (Zaitun)
Mai share hawayena shi ne abba (Zaitun)
A tabani yana nan ba zai kyaleba (Zaitun)
Komai nayi zai tafi, yace mini madalla
Bango na gida baba, uwa ita ce rumfa
Gata wahala Zaitun suna bai canzawa
Eyy 'ya ta Zaitun taso muyo wasa (Zaitun)
Tafa-tafa, yara su ke yinsa (Zaitun)
Kowa ya taba min ke zai sha casa (Zaitun)
Me zakiyi daurawa, dan kwali ko hula
Bango na gida baba, uwa ita ce rumfa
Gata wahala Zaitun suna bai canzawa
Eyy gata wahala ni 'yar yarinyata (Zaitun)
Zanso magana in nayi kiyi daukar ta (Zaitun)
So baya hanani a gunki in daga murya ta (Zaitun)
Ki san dai-dai da rashin ta, kibi hanya mai bulla
Zaitun, Zaitun
Zaitun
Komai na bida Abba shi zakayi min (Zaitun)
Madadin ka a gefe wa zai maida min? (Zaitun)
In nayi hawaye kai ke share min (Zaitun)
Duniya na min dadi lilona ya shilla
Bango na gida baba, uwa ita ce rumfa
Gata wahala Zaitun suna bai canjawa
Kyautata miki shine babban burina (Zaitun)
Karfi zai aiki harma jari na (Zaitun)
Dadi nakaji in ganki a gefen na(Zaitun)
'Yata Zaitun sai kin fadi sawun 'yan talla
Bango na gida baba, uwa ita ce rumfa
Gata wahala Zaitun suna bai canjawa
Zaitun soyayya ba karya ce ba (Zaitun)
Nima kaunarki bance banai ba (Zaitun)
In na shagwabaki ba gatane ba (Zaitun)
Yawanci 'yan gata karshe suke maula
Bango na gida baba, uwa ita ce rumfa
Gata wahala Zaitun suna bai canzawa
'Yar gata na Zaitun, sannu 'yar lelen baba
Zo gefena zauna, ban son ki da yin kwalla
Written by: Nura M. Inuwa


