歌词

Toh maza
To, haba
Muje toh, kai a'a
Bismillah zana fara waka, waka da sunan rabbi Allah
Shi yayi uba gareni yayai uwa kuma yayai 'da na Aliyu
Shi yayi saman bakwai
Kuma yayi kasan bakwai
Ba ciminti ba azara ba uban da ya bashi bulo ya daura
Kuma ba wani me kwabar ciminti
Eh, toh, toh dan girma ka Allah dan izza wa'aa dan يسٓ da سَبِّحِ
Dan wutar makaranta inji Mamman
Da ishimawi dan iziya
Dan المكارو مكاران كوباران
Dan annabi masu dubun risala
Dan تألم تألم يا كونا إن هذا يرزنا ماله قصيرا albarka fana'u
A duniya aka fanke ai shawarma
Lahira chan babu gidan biredi
Ba tsire ba balangu al'qur'an ba mai dora shayi
Toh wazai je ya daura asa walakiri ya tambaye shi
Ku saurara kuji ni
Wata waka zana tsara akan wasu yan matan kasar mu
Wai basa son wakar garin mu
A'a toh wakar wa suke so
Da zasu ki al'adar garin su
Su kama ba turai yan asara
Wai wakar Hausa ce basu so ba jinja ba suwaga
A gidan chasun garin mu sunfi son Wizkid ko Lady Gaga
Haduwar gayun garin mu motarsu su sa wakar su Shaga
Ko kaga sun keto da Raga
Toh in dai ko hakane yarima lalai kwai 'ya'ya asara
Inyamurai sun damge nasu
Yarabawa ma sun kama nasu
Amma kaji mutan garin mu
Basa nunin kauna ga nasu
Toh ai Allah ba ruwan shi
Ko suna so ko suna ki
Dole mu hau shaidai ya shana
To ai wasu basa son ganin mu
Toh wanda yace bai son ganin mu
Burbudin biri jan bidin birabikon barabiskon ruguba
Didigar magarya tura kwaba-kwabai
Inji su Barmani Choge, Choge, Choge 'yar kaura
Tasu kara, kara, kara in kara
Inyo mata karan wadan ga kirara ne (iye)
Injau natakuli tatan barauta
Karau handau namijin giginya
Mai tsula, tsiyar, tasala, tsasubar, tsatsar tsakiyar, tsuka-tsukin, tsakanin, tsu-tsuburin
Kai Zango wanan magana abarta
Wanan zagin in kayi ta bana muda ruwa ai sai kiyama
Eh wanan gaskiya ne
Dan a Port Harcourt nayi zagi suna chan kazuwa ta ishe su
Har mutum tara ma sun cimma sa'i
Wallahi Allah, ni magana gadon gidan mu ce
Tun litinin in har na fara zana kai asabar sanan na huta
Allah ya bani suna nan tari gurguzu koda roka kai kaya kabar su (iye)
Eh babu shakka, ga part two zana fada kan masu shiga gonar Allah
Sun cewa wai lokaci ne, daukaka ta kusa cif ta kare
Toh ai nasan lokaci ne kusha kurimin ku kawai su o'o
Eh Allah ba ruwan sa
Indai Allah zaya baka ai bayi fada maka zaya baka
Hakama in Allah zaya kwace, bayi fada maka zaya kwace
Sai dai kaga ya kwace abar sa shi mai sama Allah ba ruwan sa
Toh ai ba wani kato mai faso bane
Kamar tafkin da ruwa ya kare
Ba alkali bane, balle ya zubo tara ka bada
Ba dan sanda bane da zai je aiki yamma ya tashi
Sai ya bari kaje gurin sa
Ya kama ka akan laifukan ka
Ya jefa ka cikin naru, naru
Jihanama kaji gidan bashirke
Written by: Adam. A. Zango
instagramSharePathic_arrow_out

Loading...