音乐视频

音乐视频

歌词

Asma'u, Ma'u ina kike?
Gani
Eh Asama'u, Ma'u kece tauraruwa kin haska idanu
Banda kamar ki a zuciya
Asma'u, Ma'u suna na in ka kira dadi ya rufeni
Babu kamar ka a zuciya
Eh Asma'u sannu masoyiya ta kece
Kallo na idanu da kin mani sai in huce
Kirar kin zanu, ke din a ta dabance
Ba wacca nakeso sai ke mai kyaun kwaliya
Eh, ni kai ne nawa tauraro ka haska
Kai nai nunawa
Iyayai sun kai barka
Bana canjawa ko za ai mini dukka
Kai ke sanyawa, kullum in yo dariya
Kowa da masoyin shi nidai ga tawa
Indai anayin kishi ke zan wa nawa
In babu biyan bashi komin ki ya zama nawa
Bana jin kyashi akan in saki dariya
Asma'u, Ma'u suna na in ka kira dadi ya rufe ni
Babu kamar ka a zuciya
Asma'u, Ma'u kece tauraruwa kin haska idanu
Banda kamar ki a zuciya
Eh garkuwa ka ce ni daman tun asali
Wa zai taba ka gani yanzu in nuna hali
Girman sa zan daina gani in sa wa ido kwalli
Inda kai ka hana a taba ni
Nima hakan zan iya
Eh, farinciki nawa kece mafari
Ganin ka shi yakesawa inji kwari
Da kin kira ni zan zo da sauri-sauri
Cikin mazaje kai daya nake ta kuri
In nayi karatu masoyiya zo ki biya
Labarin baki kunnai shi ne zai jiya
Asma'u, Ma'u ina kike?
Asma'u, Ma'u suna na in ka kira dadi ya rufe ni
Babu kamar ka a zuciya
Eh, Asma'u, Ma'u kece tauraruwa kin haska idanu
Banda kamar ki a zuciya
Written by: Umar M Shareef
instagramSharePathic_arrow_out

Loading...