制作
歌词
A yau take babbar rana
Auren sunnah na masoya
Dangi da ƙawaye da abokai
Ku zo mu yi murna
Na sa Ubangijina mai duniya
Sarkin da shi ke mani lafiya
Ya bani baiwa ga ta kun jiya
Gare shi sai dai in yi godiya
Alhamdulillah sarki ɗaya
Roko nake ka da dan juriya
Waka ta auren so zan biya
Sunnar Ma'aiki mu yi juriya
Manzon mu shi yai yi gwagwarmaya
Muke ta numfashi duniya
Har yau wadansu suke kwaikwaya
Miji da mata sun zama ɗaya
Farin ciki ya same ku yau
Kuka na mage bai wuce miyau
Zabinki shi ne aka baki yau
Idonki ya yi haske ya yi fayau
Ki soya ƙosai da ƙayau-ƙayau
Cike da murna ki ke har wayau
Duk wanda bai murna ya yi baya
Amarya kyakkyawa ce amarya
Ku tambayo ango in na yi karya
Tana da tarbiyya ita amarya
Za ta yi wa ango biyayya
Waje na girki ba ta da sanya
Mu tuka mota, mata tukunya
Mota ba ta je ba in babu taya
Gida babu gida in babu mata
Mutum babu mutum in bai da mata
Da waccan da waccan sunansu mata
Amma akwai ɗaya ta kere mata
Akwai guda ɗaya ta zarce mata
Akwai guda ɗaya ta kere mata
Mai kyau na hali ku ji manufata
Mai yin biyayya a gurin miijinta
Wannan amarya ta ciri tuta
Ana faɗarta maza da mata
Dukkan su dangi suna yabonta
Suna faɗin kyawawan halinta
Allah ya kawo ranar bikinta
Can za ta je ta fara bauta
Farin ciki yau ranarku ce
Kun zama ɗaya ba cece ku ce
Kamar da wasa yanzu taka ce
An daura aurenku amarya ce
Komai za ta yi ma idan ka ce
Kai ma ka nuna mata halinka ne
Ana faɗin kyan ɗabi'unka ne
Ni ko na ce ta yi sa a ne
Amarya kin dace miji amarya
Yana da zance ɗaya babu karya
Yana da kyawu, kuma ga wushirya
Taho ka yi mata fara'a amarya
Taso, ka taso ango
Taso, ka taso ango
Taso amarya taso
Taso amarya taso ke ma
A yau yana ta zumuɗi
Auren sunnah daɗi
Auren soyayya daɗi
Ku zo da takon faɗi
Sha zuma in kun so ku sha maɗi
Ku muke wa sarauta muna naɗi
Da tamburana na buga ina kiɗi
Ni Sharif Umar mai waƙar gidan kiɗi
Written by: Umar M Sharif

