制作

出演艺人
Salim Smart
Salim Smart
表演者
制作和工程
Salim Smart
Salim Smart
制作人

歌词

[Intro]
Mu yi aure za aga soyayya
Albishirin masu jiran mu rabu
Ƙara faɗa su jiya
Abin da wuya (Abin da wuya)
[Verse 1]
Matuƙar wahala (Abin da wuya)
Wai za mu rabu
Abin da wuya (Abin da wuya)
Da kamar akwai wahala in bar ƙaunar ki
Da kamar akwai wahala in bar ƙaunar ka
[Verse 2]
Ko idanu ba su ganin komai
Hanci shaƙar ƙamshinka yake
Ruhinmu guda
Ra'ayinmu guda
Duk abin da ka so ƙaunar sa nake
Ba kowa a cikin ƙalbi
Sai kai ɗaya da ka je ka fake
Ƙauna ta fitine ni da son ka kullum daɗa son ka nake
[Verse 3]
Kyan tafiya, waige shi ne ginshiƙin maganar
Ba ni gajiya, da faɗa wa umma ni fa ke na tsayar
Mu yi rayuwa, har ƙarshe burina da ke mu idar
Zan yi tutiya, duka alƙawarin da muka yi da ke ya cike
[Verse 4]
Ni na san magulmata, jira suke mu rabe
Ni na san magulmata, jira suke mu rabe
Wai za mu rabu (Abin da wuya)
Matuƙar wahala
Abin da wuya (Abin da wuya)
Abin da wuya (Abin da wuya)
(Abin da wuya)
[Verse 5]
In ba kai a gare ni kamar shayi ne babu suga
Ƙwallin ƙwal, na toshe kunne ba na kama zuga
Kimar sarki shi ne a gano shi saman karaga
Bayan kai ba wanda na ke so shi ne magana
[Verse 6]
Na gode kin nuna min soyayya
Zan ba ki tukwuicinki na ƙauna sakayya
Dama da zani, yanzu in ɗauke ki in goya
Auta, wa za ya taɓan ke? Hannun sa in karya
[Outro]
Hahahaha-haha
Hoho-hoho
Ey-hey-hey-hey
Ha-ha-ha
(Abin da wuya)
Wai za mu rabu (Abin da wuya)
Matuƙar wahala (Abin da wuya)
(Abin da wuya)
instagramSharePathic_arrow_out

Loading...