歌词
Eh mana
AMG boy record
Eh indai akwai yarda to akwai kauna
Na kamu na kamu da soyayya
Indai akwai kauna to akwai yarda
Kai ne maradina hubbina
Indai kina sona to ki nuna min
Farin cikin raina karki tauye min
Da sonki nai nisa karki kucemin
Bana da wani zance sai na kaunarki
So da nauyi kai zaka sauke min
Dukka laifi in naima ka yafe min
Karka mance kaine ka koya min
Duk kalaman soyayya dake bakina
Ah-hh-hh-hh-ah
Ah-hh-hh-hh-ah
Eh yau fa hubbina kinfa burgeni
Me kake kallo ni karka cinyeni
Babu komai kyau ne ya rudani
Wai me kake zance ni karka dadani
Kwalliya ta biya kudin sabulu dai
Naga kaima kabi yan sa ido dai
Ah walla kinyi kyau saina yabaki
Kama da wane bata wane ke kadai ce ta daban
Eh fannin so da kauna ba'a kai gareki
Indai za'a bincika sai an baki maki
Ke na gani a farko ba wata ta biyunki
Nima sai da na shigo ciki na fahimta
Soyayya ta gaskiya tafi kyau a zuciya
Inda rai da lafiya zamu rayu bai daya
Mai farar anniya, kai nakewa magiya
Kar muzo daban daban wata ran ka barni
Toh kwantar da hankalinki baza na barki ba
Nima baza na barka ka ba koh za'a illatani
Indai akwai yarda to akwai kauna
Na kamu na kamu da soyayya
Indai akwai kauna to akwai yarda
Kaine maradina hubbina
Written by: Auta mg boy


