歌词
[Intro]
AMG Boy Record
Eh mana
[Verse 1]
Eh, in da rabbana so ba wahala
Da ni da kai har ba magana
Haskenmu ya zarce na fitila
Sirri na raina, je ka aje in ba ka tillas nai fitina
Da an taɓa ki, ko ba ni gurin, a take yanke zan hasala
Farin cikina son ki nake (Farin cikina son ka nake)
[Verse 2]
Eh, na ji na gani so na ba ka
Ba ni ƙara kallon waninka
Zuciya tana mi ni saƙa
Har da rayuwata na ba ka
Ni ganin ki ke sani shauƙi
Zo ki ja gaban zan biyo ki
Ni gare ki ne zan yi aiki
Don muna da babbar alaƙa
[Verse 3]
Zama a so mu yi alƙwari
Ke za na yi wa albishiri
Nai mi ki kyauta ban sikari
So in na faɗi a mun uzuri
Mai shi da kan shi ya kan takare
Na yi farauta na ci gada
[Verse 4]
In na fara, zo ka gyra
In na sauke, kai za ka ɗora
Wani riba, wani asara
Wani da izza, wani gadara
Ban da mugunta, kar da mu fara
So da mugunta, babu amana
Babu amana
Eh mana
[Verse 5]
Za na so ki riƙe ni amana
Kai nay-yi wa shimfiɗa zo ka zauna
Ni na fi so da sanin ki mu gana
Na yarda don mu gujewa hiyana
Daga zuciya, ni na sallama
Kai nai wa yabo, har na karrama
Da son ki na kwana na tashi
Ni ma da son ka na kwana na tashi
Written by: Auta mg boy