Nejlepší skladby od interpreta Umar M Sharif
Podobné skladby
Kredity
PERFORMING ARTISTS
Umar M Shareef
Performer
COMPOSITION & LYRICS
Umar M Shareef
Songwriter
Texty
Ahayyeeh, ahayye amarya
Ahayye auren sunna
Ahayye soyayya
Farinciki muke ciki aure na 'kauna
Ga ango nan dashi da amarya
Nasa Rabbi wanda yai halitta ta
Wanda shine yake biyan bukatata
Yamin baiwa na rera waka ta
Kamar wasa dafari naita tatata
Ayau gashi anata gane murya ta
Idan na rera adinga shaukinta
Ga amarya nan da ita da angonta
Umar M sharif nazo da baitin ta
Auren so an 'daura
Ga dangi sun tara
Manya harda yara
Masoya
Waka ni na rera
Baitoci na tsara
Kuzo duk ku sara
Magoya
Auren sunna yau shi aka 'daurawa
Soyayya sanadi tayo hadawa
Ga dangi nan sunata takawa
Da murna kowa yake ta nunawa
Ana ta rawa bawanda ke ta sare wa
Harda naira kowa yake ta likawa
Fatan alkairi ake ta sanyawa
Ku zauna daram babu warewa
Ai lallai kun caba
Ku zauna ku saba
Sai mutuwa zata raba
Masoya
Ku duba ku duba
Sunyi kama na duba
Ba 'karya nayo ba
Gaskiya
Kunyi farinciki da wannan rana
Yazam dole gunku nuna
Allahu ya 'karo pahimtar juna
A tsakaninku lafiya ku zauna
Hakuri wajibi idan da so 'kauna
Allahu ya kore sharri fatana
'ya 'yan ku ku haifi har nazo suna
Rannan inzo in rera baiti na
Kunyo auren sunna
'yar nune ta nuna
Shin waye zaya hana masoya
Tarkon so kunka 'dana
Kun kamo zaku gina
Kuyo rukon amana, soyayya
Ka dace da amarya ango ka dace
Kin dace da miji amarya kin dace
Naji anata yabon hali naku kun zarce
Ga hakuri a gareku hakan ai baiwa ce
Mai hakuri zai dace
Mai 'karya ya kauce
Mai nema saiya dace masoya
Mai kyauta zai zarce
Mai rowa ya 'bace
Allah yasa mu dace da masoya
Lyrics powered by www.musixmatch.com