Texty

An ce, "Ido ne kofar zuciya" Ni ko nace, "Tsaya" Ko ba ido so na shiga Zuci ya kewaya Shi so ruhi ne dashi Kira shi da yanayi Makaho ma na nan dashi Kuma babu ido garai Kamar kayi imani a ce jikin ka da hankali Yanayi ke gwada hankali ga mai shi inda shi So don Allah shine so ba son zamani ba Dama baka gane wai wake son ka da gaskiya ma Ammah in kayi dacen so baka shan wuya ma Domin wasu wai sun ce so shine rayuwa ma So ma suna ne kawai akwai shi a ko'ina Soyayyar ce gaskiya samun ta yake wuya Akwai fake itama na kula domin wasu na saya Kauna ce ba a saya matukar in ta shiga Kaunar ma ta gurin uwa ita ke karko ashe Kowa rassa mahaifiya abin ayi tausayi In ko tana nan duk ku ji wata dama ce ashe Aljannah take lahira duniya kuma arziki Domin kusan darajar uwa aka kago Maryama Aka sa mata kun faya kun mamakin haihuwa Ta haifi Isa Almasihu babu aure ba uba Kai Allah ya daukaka قُلْ هُوَ اللَّهُ أَحَدٌ So don Allah shine so ba son zamani ba Dama baka gane wai wake son ka da gaskiya ma Ammah in kayi dacen so baka shan wuya ma Domin wasu wai sun ce so shine rayuwa ma
Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out