Songtexte

Murmushi zakiman na buga tambari Ban gamon soyayya zuciya na bori Murmushi kayi man bangashen 'kauna Ban gamon soyayya zuciya na bori So mai hadari sa zuciya tadinga faman bori Fagen soyayya mun bugo tambari Iyee a gareni kin kawo farmaki Zanayo bayanai daki daki So dani dake babu shamaki Shi fure ya sakan sanyi ajiki Naita faman shauki in kina gari So mai hadari sa zuciya tadinga faman bori Fagen soyayya mun bugo tambari Tambari nakesan buga maka Ko ina kaje kazauna zan bika Inuwa ta tsamiya mu haura kuka Na hado kaya kai kabani yankin sauka Tattalin soyayya shi ya yanken jiri Eh karmu tinzira in muna kan tsauni Dan cikar masoya mu hau mizani Rayuwar mu ta riski wannan 'karni A salon soyayyar mu har muna binbini Ba'ayin sarewa koda gatari So mai hadari sa zuciya tai ta faman bori Fagen soyayya mun bugo tambari So mai hadari sa zuciya tadinga faman bori Fagen soyayya mun bugo tambari So sinadari kesa zuciya ta dinga faman bori Fagen soyayya mun bugo tambari Eh gamji dauki sara da sassaka Zan kiraka tirmi sha daka Ko buhun 'kaya wanda ba'a 'dauka Sha zamanka a rai zuciya na sanka Ni kasani a 'kalbinka karkai bari So mai hadari sa zuciya tadinga faman bori Fagen soyayya mun bugo tambari Ke tufar jiji ce adon mai dara Ni nake bayani kiyo saurara Makiyinki shi zan bugawa Gora Ban bari a kushen wacce zana aura To ki 'kara shirin rike al-'kawari So mai hadari sa zuciya tadinga faman bori Fagen soyayya mun bugo tambari Eh sanka ya shigen cikin jini har tsoka Ban gudunka da wadansu basa sanka Sai kazamma danga inzamto dirka Ga Fura ga Nono sha iya san ranka Ka zamo tauraro wanda zanba hari Murmushi zakiman na buga tambari Ban gamon soyayya zuciya na bori Eh murmushi kayi man bangashen 'kauna Ban gamon soyayya zuciya na bori So mai hadari sa zuciya tai ta faman bori Fagen soyayya mun bugo tambari
Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out