Στίχοι

So na ne fah On the beat So in akwai riya ko an kula shi baya yin karko Kuka na zuciya ban san ran da zaiyi karshe ba Kin yaudare ni yan mata Komai nake fada tabbas baza na huce haushi ba In damina tazo nasan baza a rassa raba ba Zan dauki kaddarar so ne baza na maki komai ba Kin sauke alkawar wanda mukai har gaban yi nema Tamkar bana gani bana ji na tai kai ruwa rana Samun ki ne kawai shi zai zamto cikar muradi na Sirri da naki ne kinsan komai da ke cikin rai na Ni so na gaskiya nai maki ban taba miki karya ba Har kin manta lokacin da bana manzgon ki kika zo birni Wai yanzu kin kile babu abokin fadan ki sai dai ni Karshen munafuki jin kunya jeki ba ruwana ni Zaki da na sani amman nidai ban maki fata ba Tsintaciyar mage anka ce bata mage na gano Idan naji sirrin kan nan da kike boye mini an tono Allah bamu lafiya ni na aure wutar da kin kunno Na gode rabbi ban zama kaza mai ci ta goge baki ba Nan zana barki yan mata Dubi kalar ki kowa sai dada kauna yake Kin yi kibar ki nikuma sai dada rama nake Banda ta cewa tunda hakan kaddara ta take In banda kuka zuciya bansan mi zanyi ba Kin aje kauna zaki biye rudin duniya Kin mini barna zuciya amman ya na iya Ya kika so nayi akan ki dan aka min tambaya Nayo tunannin sai dai in mutuwa ta raba Nan zana barki yan mata
Writer(s): Sani Ahmad Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out