Στίχοι

Ina jin dadi Eh ina jin dadi (Sonane fah) Ina jin dadin so Ina jin dadi Nima ina jin dadin so Ina jin dadi Ina jin dadin so Ta nai min dadi Idan na same ki a so bai zama nayi laifi ba Ina jin dadin so Ta nai mini dadi Idan na same ka a so bai zama nayi laifi ba Ko zani da nisa, bazan je bake ba Bakya da makusa, ya so bazan yi dake ba? Jinin mu gamo yayi, so bai kauce rabo ba Gasan mu dake yayi nisa bai dashe ba Yau dani ake soyayya banyi rako ba Na kamu da so ina da dalili na bana shiriri ta ba Ina a ciki can cikin so ban zama daban baya ba Kana darasi kayi bayani yaya bazan karu ba A barni da kai na yarda bazan tarayya da wani ba Zo kalli jiki na so bai sa nayi rama ba Mai son ya raba mu da kai baza nayi masa kara ba Da kai nafi tunkawo yaya bazan jajirce ba Nayi ciwo na kwanta nasan zaki ban magani Laifi in nama zaka yafe nasan zaka min lamuni Nasan zaki kare mutunci na in anyi min razini Nima zaka kare mutunci in kayi haka kayi rawar gani Da akwai magana a cikin zuciya ta, na dade ina sunsuni Nima na dade ina so na furta kunya ce bata barni ba In mun cire son zuciya Zamu zauna lafiya Sannan mu hada da hakuri A gefe mu dauko dauriya Toh kin ji ki bi a sannu Kaima kaji ka bi a sannu Ni mai daura ki a hanya ne Ba mai cutar dake ba
Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out