Lyrics
Zare-zare da abawa
Soyayyar mu bata kare ba
In babu ke bana motsa ba
Ni da ke munzam zare da abawa
Zare-zare da abawa
Soyayyar mu bata kare ba
In babu kai bana motsa ba
Ni da kai munzam zare da abawa
Hakan take, soyayya dani dake
Juna mun rike, sam-sam bamu farrake
Mun tsarkake zuciya haske take
In an bani ke, an faranta zuciya hoo-oh
Ka so a so ka shine farin ciki
Zurfin ciki na sa bakin ciki
Gidan biki taron farin ciki
Namu na zuwa inda rai da lafiya soyayya
Zaman lafiya mai sanya dariya
Dawainiya ke zanwa ke daya
Zinariya kin haske zuciya
A duniya zan so muyo zaman soyayya
Zare-zare da abawa
Soyayyar mu bata kare ba
Zare-zare da abawa
Soyayyar mu bata kare ba
Ruwan ido nasa dana sani
Kayi mini dangin mu sun sani
Farin gani tauraron zamani
Ina yini, na gaishe ka kai daya masoyi na
Dake nake soyayya ta zahiri
Alfahari dake nake cikin gari
Adon gari ke nake ta nazari
Kinyi kokari tunda ke kike ta mini soyayya
Na sallama, kaina na bar maka
Ruwan zuma na sha na miko maka
Babu gardama komai zanyi maka
Nayi harma kai kadai zanyi wa soyayya
Zare-zare da abawa
Soyayyar mu bata kare ba
Written by: RR