Vídeo musical
Canciones más populares de Arewa Vibes
Créditos
COMPOSITION & LYRICS
Hamidu Yusuf Halidu
Songwriter
Letras
(Amude on the beat)
Nayi shirin bin sahu na dau niyya
Dan Allah mai sauraro kuma ga cikiya
Zan zayano kamaninta don dubaiya
Ka dauki alkalami zana in zaka iya
In fado ma sufufin bazana kosa ba
Karshen labarin da nake bamu hadu ba
Kuma na dage neman ta nake bangaji ba
Shekaru goma masoya na jira ba'a gaji ba
Ayi hakuri masoya a'a badan ni ba
Ku gyra zama labarin ban faro ba
Tafiya ce nake tayi mai nisa
Ban san ina zani ba ni na nausa
Ga zuciya nata fadin karda in fasa
Ina tafe nai karo da Dan Musa
Yaso idan huta
Ni ko nace, "Ban gaji ba"
Allah ya kyauta haka zuciya take cewa
Bari mana sai kun saba kafin shakuwa
Abunda danaso da ki gane
Ke kinyi mantuwa
Tace akwai labarinta mai rikirtarwa
Danaji labarin da tafiyar banyo ba
Tafiya nake nisa nai karawa
Na wuce Gombe
Yanzu na shigo Adamawa
An kira sallah
Na dakata nayo tsayuwa
Nauyin dake kaina sallah inyi saukewa
Banjin dadin lokacinta yayo banyo ba
Garin Fulani ne Adamawan Yola
Nace amanar kyawu akai garin Yola
Naga Lubabatu yar mutanen Yola
Taji labarina har tana zubar kwalla
Tace dani a soyayya banga komai ba
A rayuwa lalai naga abun mamaki
Iye a soyayya babban daki
Nayi gamo a soyayya naiyo dauki
Ni nai zaton soyayya da akwai zaki
Na dandana sai naji akwai wani sirki
Da dandano nima ban tantance ba
Toh ko ke dai aljanace in ganki
Mu hadu dake labari kibani in baki
Tun randa na ganki nake son
In sake kallonki
Sai naji tashin muryar nan mai zaki
Naji ance, "Juyo"
Sai naji kamar bani ba
Writer(s): Hamidu Yusuf Halidu
Lyrics powered by www.musixmatch.com