Paroles

Hafsa kunga sarauta ce da gaske Hafsa yau jita ke nayi wa wake Hafsa tashi ki taka nan a take Zuciya da amana Hafsa dauke Zuciyar mai ciwo Hafsa wanke In duhu ya ratsa Hafsa haske Mai abin mamaki Hafsa kenan Mai karatun boko malamar nan Gun rikon addini Hafsa na nan Mai masoya da yawa jarumar nan Tashi Hafsa ki juya ba irinki Kai nuwa daga Allah yaifa saki Mai fada da cikawa Ina kiran ki Ko cikin danginki ana yabaki Daukaka daga Allah yana daga ki Tun kina yarinya irin halin ki Yanzu zana yi waka ta gimbiyar mata Hafsa mai alkhairi ke kiranta Mai rawa kayi rawa ina kidan ta Zamani ne nata ina yabata An gwada an gane bata cuta Bata kallon makiya in sun taba ta An buga an barta yanzu gata Dogaron ta da Allah ya tsare ta Walkiya ta haska bangaren ta Munga hasken hafsa mai zumunta Ko ruwa ya kawo zai tsaya ta Baya cinye Hafsa baya jan ta Ko wuta ta kama ta kashe ta Gaskiya ce doki ta rike ta Duk kadangar sharri ta tare ta Zuciyar alhari ne nufin ta Mai rubutu ita yau zai rubuta Mai karatu Hafsa zai karanta Hafsa ba matar yara bace ba Hafsa ba maganar karya take ba Hafsa ba layin boka take ba Hafsa ai ba mummuna bace ba Hafsa ba kin al'umma take ba Amsa sunan ba wasa bane ba Tunda ba kowa za'ayi kira ba Sai su wance da wance kunji babba Yanzu jirgin sama yazo ya sauka Hafsa shiyayi niya zaya dauka Gashi jirgin ruwa yazo iyaka Hafsa shi zai sauke bata tamka Sannu baiwar Allah Hafsa kenan Rayuwa tayi kyawu duniyan nan
Writer(s): Ali Isa Jita Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out