Isah Ayagi के शीर्ष गीत
इसी प्रकार के गाने
क्रेडिट्स
PERFORMING ARTISTS
Isah Ayagi
Performer
COMPOSITION & LYRICS
Isah Ayagi
Songwriter
गाने
Ai hakuri
Dan mai hakuri na tare da Allah
Kai jumuri
Shi mai jumuri zai samu kamala
Rabo naka ne
Babu mai tsaida shi
In ya riga ya fita
Babu mai dawo shi
Toh kuji wanan
In Allah ya kare ka
Toh ba mai iya 'bada ka (kwarai)
Duk mai kudurin cuta
Gareka dole ya kyale ka (dole)
Ka rike sarki Allah (kwarai)
Ka kama رسول الله (صلى الله عليه وسلم)
Koh asiri ko tsafi
Baza suyi tasiri ba
Allah gyra
Ya Allah gyra (Allah gyra)
Ga wasu fatan alkairi
Wasu koh na fatan sharri
Kuyi hakuri makiya na masoya
Wata rana sai labari
Na yarda da Allah kai ke yi
Ba wani ba kai ba
Kaine ka aje ni a inda nake
Koh ban zaba ba
In kaso kana iya sauya min
Koh ban nema ba
Kamar yadda kayini mawaki
Watakil shine mafi alkairi
Ga wasu fatan alkairi
Wasu koh na fatan sharri
Kuyi hakuri makiya na masoya
Wata rana sai labari
Wasu na kushe wasu na zagi
Wasu na aibanta mu
Mun yarda da Allah dai ne
Su ko suna kafurta mu
Kuma basu da wuta da aljanna
Balle su saka mu
Muna neman su da alkairi
Suna neman mu da sharri
Ga wasu fatan alkairi
Wasu koh na fatan sharri
Kuyi hakuri makiya na masoya
Wata rana sai labari
In Allah ya kare ka
Toh ba mai iya 'bada ka
Duk mai kudurin cuta
Gareka dole ya kyale ka
Ka rike sarki Allah
Ka kama رسول الله
Koh asiri ko tsafi
Baza suyi tasiri ba
Allah gyra
Ya Allah gyra
Ba zagi muka zo ba
Sai fatan alkairi
Wasu na nan sudai fatan su
Su gan mu muna fama
Su gan mu a gajiye mun kasa
Muna neman dama
Toh kuyi hakuri mun rike Allah
Zai mana alfarma
Mu bamu neme ku da sharri ba
Mu daku Allah sa muga alkairi
Kai hakuri
Dan mai hakuri na tare da Allah
Kai jumuri
Shi mai jumuri zai samu kamala
Rabo naka ne
Babu mai tsaida shi
In ya riga ya fita
Babu mai dawo shi
Allah duk mai jin haushi na
Ya rabbi ka yafe mai
Mai hassada agreni
Abinda kamun shima kai mai
Inka bashi abinda ka bani
Ina rokonka ka ninka mai
Inje in taya shi da murna
Nai mai fatan alkairi
In Allah ya kare ka
Toh ba mai iya 'bada ka
Duk mai kudurin cuta
Gareka dole ya kyale ka
Ka rike sarki Allah
Ka kama رسول الله
Koh asiri ko tsafi
Baza suyi tasiri ba
Allah gyra
Ya Allah gyra
Ba zagi muka zo ba
Sai fatan alkairi ne
Isah Ayagi ne
Writer(s): Isah Ayagi
Lyrics powered by www.musixmatch.com