Video Musik

Video Musik

Dari

PERFORMING ARTISTS
Malam6ix
Malam6ix
Vocals
COMPOSITION & LYRICS
Sulaiman Iliyasu Saeed
Sulaiman Iliyasu Saeed
Composer
PRODUCTION & ENGINEERING
Hassan D YP (BOY)
Hassan D YP (BOY)
Producer

Lirik

[Intro]
Malam6ix
Maryam A sadik
Mad oh!
[Chorus]
Ina son ki don Allah kar ki musawa
A Lailatul kadari na, ke zana roka
Ina son ka don Allah kar kai musawa
A Lailatul kadari na, kai zana roka
Ina son ki don Allah kar ki musawa
A Lailatul kadari na, ke zana roka
Ina son ka don Allah kar kai musawa
A Lailatul kadari na, kai zana roka
[Verse 1]
Soyayya soyayya ce
Taki daban na banbance
Tun yarinta na makance
Bana ji na kurmance
Tuntuni kai ne zabi na
Ka cancanci tukuici na
Ungo guri zo nan zauna
Ga ajiya dau ruhina
Kalma ta ratsa ni
Harufan so sun huda ni
Ko zargi zai daure ni
Kyan hali sai ya kwance ni
Son ka, ka ke dada rurawa
Jini yake dada ratsawa
Kwakwalwa tai ganewa
Zuciya tai sabawa
[Chorus]
Ina son ki don Allah kar ki musawa
A Lailatul kadari na, ke zana roka
Laylatul kadari na
Laylatul kadari na
Laylatul kadari na
Laylatul kadari na
[Verse 2]
Ba dama incanza ka
Da amana soyayyar ka
Inuwa ta inuwar ka
Ya zan yarda a kwace ka
Wai nayi hauka ake cewa
Nace fade ma batawa
Kan ki na gama zarewa
Kuma ba ranar dawowa
Dadi soyayyar ka
Na sha ta kai mun ka
Ba sauki samun ka
Na gane muhimmancin ka
Allah yai mun kyauta
Dole na kare mutumcin ta
Yanci na na kwata
Na karbo soyayya ta
[Chorus]
Ina son ka don Allah kar kai musawa
A Lailatul kadari na, kai zana roka
Ina son ki don Allah kar ki musawa
A Lailatul kadari na, ke zana roka
Laylatul kadari na
Laylatul kadari na
Laylatul kadari na
Laylatul kadari na
Laylatul kadari na
Kai zana roka
Laylatul kadari na
Ke zana roka
[Outro]
Dadi soyayyar ka
Na sha ta kai mun ka
Ba sauki samun ka
Na gane muhimmancin ka
Allah yai mun kyauta
Dole na kare mutumcin ta
Yanci na na kwata
Na karbo soyayya ta
Promix
Written by: Sulaiman Iliyasu Saeed
instagramSharePathic_arrow_out

Loading...