Video musicale
Video musicale
Crediti
PERFORMING ARTISTS
Hamisu Breaker
Performer
COMPOSITION & LYRICS
Hamisu Breaker
Composer
Testi
Gangar kiɗan na manuyan mata ne
Sannan batun da zan na iyaye ne
Breaker akwati mai zance ne
In ji Faruku Medium na sarkin waƙa
Ya Allah dafa mini ka san ba za na iya ba
Ya mai iko kai ke kyauta da ba ka karɓa
Ya sarkin mulki ba ni yau na zazzaga zance
Yau wakar ta iyayen da ba su yin rowa ce
Maʼana ta iyayen amarya kun ji ƙarshen zance
Masu kyautar ʼya in na yo kuma hadiyya ce
Ya Rabbi ka ninka salatin Ɗaha ƙarshen ƙarshe
Sidi gatan kowa ka ji farkon tushe
Ya kafa musulunci sonsa ne kawai dacewa
Maman amarya fito na ba ki babbar ganga
Kin san dole na mi ki taho da takun burga
Maman amarya fito na ba ki babbar ganga
Kin san dole na mi ki taho da takun burga
Kin kai a yaba miki uwar da ba kushewa
Mamana a gun biki nake dubawa
Na ganta a zaune a rai na in ji tana haskawa
Idan na tuno ta haifi ʼyar ta za su rabewa
Sai in ji tausayi na mama ya kama ni
Ku tuna daukar ciki da haihuwa sai mama
Ku tuna raino, zama ji,in uwa sai mama
Ku tuna juyi, kiriniyar ɗiya sai mama
Mama sannunki a jinjinawa mai alfarma
Mama kenan in snar da ke abin burgewa
Ke kike zamo farin wata da ke haskawa
Tarbiyyar ʼyaʼya mama ke ake kangawa
Mama mai haƙuri ga mu yau cikin fadarki
Yau nai aniya na zage damtse sai na gaida ki
Sannu uwar amarya ga jinjina ta gun ki
Salisu Yaro ɗauki alkalam ka rubuta
Komai na fada sai ya zamma ka nanata
Tafiya da gwani daɗi gare shi ga kalmata
Yau dai uwa amarya nake yi wa waƙata
Yanzu mahaifin amarya za na komo gun ka
Wasu baituka ne na girma za na miko gun ka
Ka kai a yaba maka da hikima son barka
Ka ga mazan jiya za ki fama mai yiwa kowa
Amarya ki duba ga mahaifi na ki yana ta yin ruwa
Buri nai a fita kunya na gai da kai baba
Abin a yi murna baba yana darawa
Mun sha aiki, Baba an sha aiki
Tudun kan tafki, yau na yi maka maki
Yau ake gama aiki an yi bikin ʼyar kirki
Ke amarya gare ki, yau dai sai an kai ki
Share kukanki ba mai ce in sakarki
Ki kwana gidanki ki narke, to mama gare ki na dan fake
Na kawo tsaraba ga ke, mai abin ji ne ga ke
Da ke da miji na ki har bude murya nake
Wani taku dai nake, har wani taku dai nake
Sai wata rana, na bar ku ʼyan uwa
Umma ga sako na mama ina nan zan kuma dawowa
Written by: Hamisu Breaker