album cover
Afra Jingle
1108
Afro-Pop
Afra Jingle è stato pubblicato il 27 aprile 2018 da Abnur Entertainment come parte dell'album Ma'aurata
album cover
Data di uscita27 aprile 2018
EtichettaAbnur Entertainment
Melodicità
Acousticità
Valence
Ballabilità
Energia
BPM123

Crediti

Testi

[Intro]
Eh yau ku fito da labari na zo
Idanuwa na ta ganin hazo
Nai godiya ga duka ʼyan Gwangwazo
Domin ban raina kallarsu ba
[Verse 1]
Dukkanin yabo da godiya su tabbata ga Ubangijin Hallita
Wanda yai dare yai rana
Yai halitar ʼyan adam maza da mata
Ya dasa mana so da ƙauna a cikin zukatanmu
[Verse 2]
Wannan ya sa ba ni da abin tinƙaho
Sai masoyana
Kullum burina in nishaɗantar da ku
In faranta muku
Da irin waƙoƙina kamar yadda kuka saba ji
[Verse 3]
Yadda na ke son ki
Ki ka bar ni ina zan sa kaina?
Na bayyyana miki sirrin safe da rana
[Bridge]
Duk a cikin sabon album ɗina mai zuwa
[Verse 4]
Na ba ki amanata
In na tafe baya nake hange (A dare)
Da akwai matsala babba
Gun mai tafiya da rashin waige (A dare)
[Bridge]
Sunan album ɗin "Afra"
[Verse 5]
Lokaci ne ya haɗa shi za ya raba
ʼYan makaranta daɗi
Sauran ɗalibai yau dai ga Afra ta nai muku bankwana
[Verse 6]
Kanki ina shauƙi
Kana ina fatan alkairi
In ki ka raɓe ni na dace dan ba kya sharri
Alfaharina ne wacce nake so ba ta buri
[Bridge]
So ya taɓa ka?
Ka san zafinsa?
Ko daɗinsa ka sani?
[Verse 7]
A gaskiya na sha wahala ta so
Sirri na zuciya zan fallaso
Na samu rangwame na rage kaso
Ƙauna ba zan daina ta ba
[Outro]
Ku nemi album ɗin "Afra"
Za ku ji abin tausayi da na mamaki a cikinsa
Ku jira zuwansa
Zai zo muku in sha Allahu
Written by: D.R., Nura M. Inuwa, RR
instagramSharePathic_arrow_out􀆄 copy􀐅􀋲

Loading...