Testi
It's Ahmerdy
(Sultan with the beat baby)
Hajiya diyar ta ki ta girma
Amarya yau fah ranar ku ce (Son barka haka)
Amarya yau fah ranar ku ce
Hajiya diyar ta ki ta girma
Amarya yau fah ranar ku ce
Bikin aure muka zo
Murna muka zo fah muyo
Wanga rana mun dade muna jiran ta
Amaryan mu tafi ta kowa
Kyakkyawa duba
Ai ko da kudin ka
Sai da rabon ka
Amaryan mu fes-fes-fes
Angon ta fes-fes-fes
In ka duba soyayya tayi rana
Taro yayi taro
Taro da masoya
Yan uwan mu, yan uwan mu
Yan uwan mu, yan uwan mu
Biki yayi biki
A yau da dangi muka yo
Ga yan uwa duk sun zo
Ga yan uwan mu, yan uwan mu
Yan uwan mu, yan uwan mu
Mai kalangu kazo ka ban kidan amarya
Babu mamaki kurna tayi kamar magarya
Burin hajiya a kaiki daki kiji amarya
Wataran fah in zo, muzo musha miyar amarya
Amarya taho
Don Allah waigo
In baki waigo ba amarya zan hada kaya na na koma
Ango waigo
Don Allah waigo
In baka waigo ba ango zan hada kaya na na koma
Yau biki yayi biki
Gidan biki sai shagali
Ga iyaye
Ga iyayen amarya muna maraba
Ga iyayen ango muna maraba
Ango da amarya sun fito a tare
Gasu kaman masoyan farko
(Eh mana!)
Hajiya diyar ta ki ta girma
Amarya yau fah ranar ku ce
Hajiya diyar naki na murna
Amarya yau fah ranar ku ce
Amarya ce, amarya ce
Amarya
Amarya ce, amarya ce
Amarya
Amarya ce, amarya ce
Amarya
Murna duka muke tayi amarya
Writer(s): Ahmad Gambo Salman
Lyrics powered by www.musixmatch.com