Video musicale
Video musicale
Crediti
PERFORMING ARTISTS
Salim Smart
Performer
PRODUCTION & ENGINEERING
Salim Smart
Producer
Testi
[Intro]
Ah, ku yarda a kan soyayya
Zero tension ne ni
Wanda nake ƙauna
Ba ta sanya idona kuka
[Chorus]
Ku yarda a kan soyayya
Zero tension ce ni
Wanda nake ƙauna
Ba ya sanya idona kuka
[Verse 1]
Na san na more
Na kere sa'o'ina
Kuma na dace
Na tantance mai sona
[Verse 2]
Kin kore
Kin share ɓacin raina
Kuma kin nisanta ni
Da kewar soyayya
[Verse 3]
In ya juye yan da na so
Maƙiya ko ba sa so
In dai Allah zai so
To wataran ni ce matarka
[Verse 4]
Kin riƙe umarnina
Kin iya dokokina
Na mallaka miki kaina
Ba ni bari ki yi kuka
[Verse 5]
Na yi gamo-da-katar a so rabbi ya gama saya ni
Wadda nake so tattalina kamar ta goya ni
Komai nisa ba ta gandar tashi ta ishe ni
Ni ʼyan mata saboda wannan ba sa birge ni
Ko ban faɗa ba, za ku yi sheda ne
Ko ban faɗa ba, za ku yi sheda ne
[Verse 6]
Ya iya rarrashi, mai sona na musamma ne
Fara'a ko yaushe, in ya yi fishi da dalili ne
In so makaranta ne, kai malamin Mathematics ne
Ka iya lissafi, don ka harbe ni a angle ne
Sonka ya yi mini tasiri ne, ya yi min zaune
Ya kewaye min zuciya ya dasa min ƙauna
[Chorus]
Ah, ku yarda a kan soyayya
Zero tension ne ni
Wanda nake ƙauna
Ba ta sanya idona kuka
[Outro]
Ku yarda a kan soyayya
Zero tension ce ni
Wanda nake ƙauna
Ba ya sanya idona kuka


