album cover
Kece
23.398
World
Kece è stato pubblicato il 5 aprile 2018 da Apple Media Africa come parte dell'album Iconic Sounds of Africa, Vol. 67
album cover
Più popolari
Ultimi 7 giorni
00:00 - 00:05
Kece è stata scoperta più frequentemente nei primi secondi di la canzone durante la settimana passata
00:00
00:20
00:35
00:40
01:05
01:10
01:25
01:30
01:35
01:40
03:20
00:00
03:27

Crediti

PERFORMING ARTISTS
Hamisu Breaker
Hamisu Breaker
Performer
COMPOSITION & LYRICS
hamisu said yusuf
hamisu said yusuf
Composer

Testi

Eh a duniya ke kika zam farin cikina
Idan ba ke wa zana bai wa kauna?
Farin cikina kin zam jinin jikina
Idan da so kauna ba ta kaini rana
Kin zam jigo hasken idaniya ta
In na rasaki wa zata bani gata
Ni ke nake wa kallon sarauniyata
A gurbin zuciya bani aje wata
Ki dawo inda nake dan mu zanta
Mai sona mai kyan hali nagarta
Baiwar Allah ke ce cikar muradi
Wanda ke sonki na so shi dan zumudi
Ki mini uzuri kar kice nayi kaudi
A kanki ko meh nayi so ya ingizani
Idan na zauna de ke nake tunani
Ko cikin Bazara damina da raani
Wayyo Allah da ma zaki tunani
Kamar yadda nake miki sai ki so ni
Idan na kalle ki kina rikirkita ni
A zuciyata ina sonki ba ma'auni
Bani daama ya masoyiyata
Mai rabon ya ga badi zai gani gwanata
Cikin masoyanki a yanzu nayi rataa
Tunda ni zan iya baki rayuwata
Taho garen zana rikeki ba mugunta
Ni fa nace kece masoyiyata
Abin da soyayya ta sanar aminta
Tausayi ko ko zamanmu kai da fata
A gidan duniya samun masoyi dadi
Rashin masoyi shi ke cire nishadi
Da kin kirani nan take zani amsaa
Aurenki nai niyya kar kice na fasa
Zaki zam matata wai ya kunsaa
Duk kamanni naki sunyi ba mabusa
Walwalata abar alfaharina
Sonki yai mini dauri irin na gwarmai
Ni fa sonki biyayya kawai nake mai
Sonki yai mini dadi inai da mai mai
Ni ban da burin da ya kai in baki komai
Wande ke kinki a yanzu zani far mai
Nafada soyayya ruwan Zuma ce
Wassu na kallo na kamar a zauce
Darrajar soyayya ko ba kwatance
Wanda ke so shi ya sanshi ko a zance
Masoyiyata karbi uzzurina
Kar ki bar sonki ya zamma ajalina
Farin cikin soyayya ta zamma kauna
Wallah kan sonki kawai na manta kaina
A ko da yaushe hotonki na hanuna
Duka abin da kake so yana gareka
Ina sonki fiye da so hakan na saka
Abin da ranka yake so idan ya so ka
Yana da daadi ni haka nan na dauka
Shiyasa soyayarki tai ta girma
A zuciyata komai ta fishi kima
Written by: hamisu said yusuf
instagramSharePathic_arrow_out􀆄 copy􀐅􀋲

Loading...