album cover
Dama
1
World
Dama è stato pubblicato il 24 aprile 2018 da Apple Media Africa come parte dell'album Iconic Sounds of Africa, Vol. 76
album cover
Data di uscita24 aprile 2018
EtichettaApple Media Africa
Melodicità
Acousticità
Valence
Ballabilità
Energia
BPM100

Crediti

Testi

Dama tana zowa mutum sau 'daya sai muyi hattara
Ilimi mizanin rayuwa in nusheka
Dama tana zowa mutum sau 'daya sai muyi hattara
Ilimi mizanin rayuwa in nusheka
Rayuwa makaranta wani ya dace wani bai dace ba
'Dauketa a kasuwa wani yaci riba wani bai samu ba
'Dauketa a yaki wani ya tafi wani bai dawo ba
Wani nata dariya wani ko na kuka
Dama tana zowa mutum sau 'daya sai muyi hattara
Ilimi mizanin rayuwa in nusheka
Yarinta duba nazari kadinga kulawa
Kaci riba malam kafin tsufa yayi zowa
'Kuruciyar ka rayuwar ka kayi ginawa
Yarinta inta wuce bata dawowa gunka
Dama tana zowa mutum sau 'daya sai muyi hattara
Ilimi mizanin rayuwa in nusheka
Dama ka samu ta kudade kokwa sarauta
Kayi kyawun hali malam maza nuna nagarta
Arziki kayi kyauta gun mulki kar kayi cuta
Dama ce aka baka wataran naga waninka
Dama tana zowa mutum sau 'daya sai muyi hattara
Ilimi mizanin rayuwa in nusheka
Lafiya in bata gun ibada kai nitsawa
Kayi bautar Allah lafiyar ka ingantawa
Duniya da 'kiyama arzikinka kai nemowa
Ranar da babu lafiya saidai ayi jaje gunka
Dama tana zowa mutum sau 'daya sai muyi hattara
Ilimi mizanin rayuwa in nusheka
Dama tana zowa mutum sau 'daya sai muyi hattara
Ilimi mizanin rayuwa in nusheka
Iyaye hakika matsayi nasu yafi kwatance
In munyi biyayya a garesu fa zamuyi dace
'Yan samari buri zance ku amince
Bayan Allah da ma'aiki iyaye ne a gaban ka
Dama tana zowa mutum sau 'daya sai muyi hattara
Ilimi mizanin rayuwa in nusheka
Ummi na gode tarbiyyarki kin 'daurani
Kin fifita ni kullum guna kika nuni
Innayo kuka ba bacci kin goya ni
Sata a cikin Aljanna Allahu dan manzonka
Dama tana zowa mutum sau 'daya sai muyi hattara
Ilimi mizanin rayuwa in nusheka
Written by: Mahmud Nagudu
instagramSharePathic_arrow_out􀆄 copy􀐅􀋲

Loading...