クレジット

PERFORMING ARTISTS
Ahmad Shanawa
Ahmad Shanawa
Performer
COMPOSITION & LYRICS
Ahmad Shanawa
Ahmad Shanawa
Songwriter

歌詞

[Verse 1]
Ahmad Shanawa
Baban chakwai
[Verse 2]
Ashe gaskiya tana da dadi
Ashe gaskiya tana da daci
Ashe gaskiya tana da rana
Makaryaci ba za ya yi dace ba
[Verse 3]
Makaryaci ba za ya yi suna ba
Ko da ya yi ma ba zai tasiri ba
Ni ba gida ba ni ba mota ba
Ba mai tara dukiya masu yawa ba
Babana shi ba gwamna ba
Ba shugaba kasa ba ba kuma memba ba
[Verse 4]
Ban je makaranta mai tsada ba
Ban je Dubai ba kumma ban je Landan ba
Gidanmu ba a GRA ne ba
Ban dauki selfie na sa Instagram ba
Ko zana zamma saniyar ware
Wallahi ni ba zani zam makaryaci ba
[Verse 5]
Ashe gaskiya tana da dadi
Ashe gaskiya tana da daci
Ashe gaskiya tana da rana
Makaryaci ba za ya yi dace ba
[Verse 6]
Na fada a rijiyar soyayyarta
Cikin dare ina ta tunaninta
Na dau waya na leka shafinta
Na Instagram har ma da Twitter
A nan na kalli dukkan hotonta
[Verse 7]
Nai na'am da kyawun surarta
Nai DM na ce kin hadu 'yan mata
Tai godiya nai requesting lambarta
Farin ciki ya kama zuciyata
Ji nake yi kamar ba nine ba
[Verse 8]
Ashe gaskiya tana da dadi
Ashe gaskiya tana da daci
Ashe gaskiya tana da rana
Makaryaci ba za ya yi dace ba
[Verse 9]
A hankali muka yi sabo da juna
Muna waya da ita ba dare ba rana
Ta ce Babanta wani hamshaki ne
Dan kasuwa a Dubai can yake zaune
Tana zama garin Abuja ne
Sun zo da Mamanta ganin Kakanninta ne
[Verse 10]
Kullum ta dauki hoto mai kyau
Ta sa Instagram zato na gidansu ne
Idan ta dauki hoto mai kyau
Cikin mota ma ashe na saurayinta ne
[Verse 11]
Idan ya kai ta don su shakata
Ta dau hoto sai ta sa sweet home ne
Ashe Babanta dattijo ne
Mai sai da goro bakin layin sarki ne
Mamanta mai neman na halali ce
Kosai take siyarwa da kunu ba cincin ba
[Verse 12]
Ashe gaskiya tana da daci
Ashe gaskiya tana da rana
Makaryaci ba za ya yi dace ba
[Verse 13]
Wata ran da yamma ni da abokai na
Mu ka yi sha'awar mu sha kunu da kosai
Aboki dan Muhamman yace
Ya san a inda zamu je mu sha kunu da kosai
Abin kamar mafarki nake
Sai gamu nan a inda ake yin suyar kosai
[Verse 14]
Abin da nagga ya rikirkita ni
Nan take sai jiri ya kwashe ni sosai
'Yar da tace tana garin Abuja din nan
Sai ga ta nan tana suyar kosai
A take na ciro hotonta
Muka kare mata kallo da abokai na sosai
[Verse 15]
Cabdijan
Akwai babbar matsala
Written by: Ahmad Shanawa
instagramSharePathic_arrow_out

Loading...