クレジット

歌詞

Kin bani so
Kin bani soyayya
Tsintuwa nayi a soyayya
Zuciyata tayi fari
Kyakkyawar yarinya
Ta sani cikin nazari
Nayi nisa cikin son ta
Kar ku fara kuce in bari
Burina na aure ta
Ta haifa mini dan jinjiri
Ba zan gaji a kalon ta
Tun dare har a wayi gari
Daban kike ko a cikin taurari
Kallon ki wanda yayi shi zanyi wa mari
Akan so na amince in shiga yari
Sarauniya
Zinariya
A guna kin wuce gimbiya
Idaniya
Ba lafiya
In basu gan kiba ba dariya
Da soyayya
Kin mamaya
Kwatsam na jiyo ki a zuciya
Ta jijiya kika zagaya
So da jini ya gauraya
Madubi sannu abin kallo na
A so ba mai canzan rayi na
Kullum in na dau alkalami na
Hoton ki nake aikin zanawa, tawa
Da fari da baki akwai banbaci
Ido ke ganewa
Cikin zaman da akayi adalci
Yafi dorewa
Gare ni ko rai ya baci
Kece mai yin gyarawa
Ina ta bin ki nasa naci
Kar ki guje ni taho tawa
Soyayya mai inganci
Nake miki da bata kodewa
Ki kula da ni
Zan kula da ke
Ki saka ni a ran ki
Kar ki yada ni
Bani yada ke
Jani zana biyo ki
Jani zana biyo ki
Jani zana biyo ki
Da soyayya na fito
Da soyayya zan koma gida
Son ki kadai na mato
Kan hanyar bana jin gargada
Ke, ke mulkin zuciyata
Ko a ina haka zan fada
Zan ba ki abinda na mallaka
Guna in kika bida
Ki juyo min fuskar ki induba
Tunani naki da shi na saba
Addu'ar da nake Allahu ya karba
Mu yo auren mu na so
Soyayya
Soyayya (so-yayya)
Soyayya (so-yayyal
Soyayya
Kin bani so
Kin bani soyayya
Written by: Umar M Shareef
instagramSharePathic_arrow_out

Loading...