クレジット
COMPOSITION & LYRICS
Umar M Shareef
Songwriter
歌詞
Ayeye
Oho oh-hh-hh-hh
Aha aha ah-hh-hh-ah
Na samu kudi na samu
Na shirya auren ki
Na samu kudi kin gani
Nawa ne sadakin ki?
In an daura aure
Har mota ma zan siya miki
Ki fada a duniya
Wace kasa kike so ni zan kaiki
Tunda lokaci yayi
Komai akeyi sai nayi
Akwatuna, na riguna
Na sarkuna na adon mata
Muyi hotuna, shagulgula
Ado Gwanja yazo yasa kidan mata
Kibar kuka, kibar kuka
Lokacine gashi nan yayi
Bayan wuya akwai dadi
Hakama din taimako ya zamo mana
Oh-hh-hh-hh-hh-hh
Ki daina kuka, ki daina
Ki daina kuka, ki daina kuka
Ki daina tina baya, ki bar tinawa
Kin zamo amarya, amarya tawa
Ke da karkara sai dai ziyara
Ba dakan fura fada ki kara
Kan idon su yau sun ga ishara
Sun mana sharri, ya zama alkairi
Faruwar hakan ban damu ba
Da ina gida ban fita ba
Arzikin kinka da bai samu ba
Na dauki kaddarana da sakayar Allah
Kibar kuka, kibar kuka
Lokacine gashi nan yayi
Bayan wuya akwai dadi
Hakama din taimako ya zamo mana
Oh-hh-hh-hh-hh-hh
Ki daina kuka, ki daina
Ki daina kuka, ki daina kuka
Wallahi kin rike alkawarina
Kin jure dukan wahalhalu a kaina
Inuwa mafaka ta rana
Yar halak, ni na baki suna
Har abada kina a zuciya na
Baza nayi miki kishiya ba
Waye zai taba ki a yau in gani
Duka wani gata zaki gani
Tunda yau kudi sune idon gani
Idon gani magani
Kibar kuka, kibar kuka
Lokacine gashi nan yayi
Bayan wuya akwai dadi
Hakama din taimako ya zamo mana
Oh-hh-hh-hh-hh-hh
Ki daina kuka, ki daina
Ki daina kuka, ki daina kuka
Ayeye
Oho oh-hh-hh-hh
Aha aha ah-hh-hh-ah
Written by: Umar M Shareef

