Vergelijkbare songs
Credits
COMPOSITION & LYRICS
SANI AHMAD
Songwriter
Songteksten
So na ne fa, on the beat
Shi so ruwan zuma kuma ruwan guba ne ban rasa ko daya ba
Ya zanyi ne da so, na ga duniya kai kadai take duba
Indai akwai lalura cikin jikina bai wuce kauna ba
So yadda nayi nufi wata kila ba haka zaka zomin ba
Tamkar ana kafi, in kama so bai san wata kara ba
Zai kama zuciya ya bi jijiya ma bazai tsaya nan ba
Ni dai masoyiya ta kece, jinin jikina
Inna rasa ki to zan zauce, ji lafazi na
Komai nake bida dan kece, dare da rana
Ba'a ziga ni dan in barki, babu ruwa na
So yayi gurin zama ya zauna, a zuciya na
Ni bani son ki yada amana, mu rike juna
Karki bari in shiga damuwa, tunda so nada hadari
Ke nake ambato kawai, inna zauna wuri-wuri
Ni dake munyi alkwar, baki sanya ni garari
Naga duk martabar miya, bai wuce maggi-gishiri
Dukka mai so akwai jarabta gareshi ko wanne lokaci
Kaddarar so idan ta farma sai ayi ta cema mahaukaci
Babu komai ga dukka mai yin so hakuri ne hakika ci
Tunda ma duniyar ta Allah zamanta bama da tabbaci
Kai kana son wani yana son ka kaji so mai kulafuci
Kara rudi na zuciya ya zuga mu fita hayyaci
So akwai damuwa kunji yan uwa na
Yadda Allah yaso haka zayayi min
Ahh, nagode
Writer(s): Sani Ahmad
Lyrics powered by www.musixmatch.com