Kredyty

PERFORMING ARTISTS
Nura M. Inuwa
Nura M. Inuwa
Performer
COMPOSITION & LYRICS
RR
RR
Songwriter

Tekst Utworu

[Intro]
Eh, manyan mata ni tamburanku a yanzu nake daka
Ku ko 'yan mata aikinku yau bai wucce riƙe jaka
[Verse 1]
Duniya daɗi na lura babu kamar ku uwa uba
Haka ne yassa nai muku 'yar tsarabarku ku rarraba
Yanzu ni waƙa nake yi, wasu su ji su faɗɗi ta yi
A faɗin Hausa kama da wane ba ta zama wane ba
Ɗinkin hannu idan ka ba ni ba zan iya yin shi ba
[Verse 2]
A cikin waƙa ta mata, godiya zan wa uwata
Komai za nai, ni na sani ba za na biya ki ba
Allah sarki Ya ja da ranki, akwai kallo gaba
Wataran, ba wataran ba, laifukana na yi tuba
[Verse 3]
Ita ƙasaita tilas a ƙyalewa giwa ta yi
Mai ciki ko babu naƙuda an san ta laulayi
Mai daka zai nemi turmi, fito ruwa sai da komi
Ance kanwa uwar gami ce ban musa haka ba
[Verse 4]
Gashin tsire shi ba a yinsa idan ba tukkuba
Jini na can a kwata, yin fawa sai mahauta
Tunani daban da naku idan na yi nazzari
Hanyar jirgi daban da mota fannin sufuri
[Verse 5]
Tunda ba a ado da yana, shinge kare gidana
Ana kallo yau kallabi shi ke jan rawwani
Cutar mutuwa sai haƙuri ba ta jin magani
Lissafi sai kwakwalwa, ga Salwa ga Makwarwa
[Verse 6]
Ko ba yanka kifi ana iya kamawa a ci
Shi agogo a kan saka hannu domin lokaci
Sammako ke sanya sauri, noma fari da tauri
Yanayin danshi ke sa jikin bango yai yo rima
[Verse 7]
Busa ta ƙaho da tai yawa 'yan maza sa hau tsuma
Da ganin haure katanga, an sha wahala a daga
In zan hutu na kan biɗar in yi bakin dausayi
Allah sarki tsare ni kar na yi kallon tsautsayi
[Verse 8]
Zafi ga dafin kunama, maza sun ƙwaci gulma
A buga a bari sunanki ne amara ƙirjin biki
Sai mai daraja ake faɗa wa harkar arziki
Garwashi ya ɗauki zafi, rijiyata ta yi zurfi
[Verse 9]
Mu riƙe noma rufin asiri ne gun tallaka
Mafarauci don ya kare kansa yake ɗaukar baka
Zakara in ya yi cara, ba a jin kuwwa ta kura
Kiwon shanu da karnuka ba a kai fulfulde ba
[Verse 10]
Filin dambe sai masu ƙarfi za ka gani gaba
Rannan a cikin mafarki, na ga na kayar da Gwanki
A jikin kaza da 'yan uwanta ake samun ƙuma
In ga manya su 'yan ƙanana dole su sallama
[Verse 11]
Hali ba ya kama da siffa, takalmi ya fi safa
Audiga ba suttura bace sai in an sarrafa
Nutsuwa ce za ta rarrabe mana tsaki da ƙwafa
Korama dangin su gulbi, haƙa sai da magirbi
[Verse 12]
Ita isgar Raƙumi tana sama tai nisa da ƙas
Akuya in za a mata kora ba ta gane asss
Ƙamshi ya girmi wari, ɓaure ya gaji bauri
In za a yi gaɗa, a bari sai an je dandali
[Verse 13]
Na lura baƙin jini ake gun karɓar jangali
Gatari aikinsa sara, a yawa aka samu rara
In dai ka ji Wahidi guri da akwai almajiri
Mata suke ta'ammali da siyen kayan yari
[Verse 14]
Wata ta kerewa tsara, a gurin wata ba dabara
Hadari in ya haɗo samanıya za ka ji ruggugi
Allon kallo maza na dauri su kan ce majigi
Gyaɗa ta juri ɓara, a kwashe tuwo da mara
Manyan mata dominku nai waƙar nan na fada
Written by: RR
instagramSharePathic_arrow_out

Loading...