Tekst Utworu
Dace ni nayi akan soyayya na more
Dace ni nayi akan soyayya na more
Ke nafi so kin zam zabi na
Samun ki ya zama cikan buri na
Hoton ki na kai wa gida dangi na
Kowa ya duba
Abokai sun duba
Amsa suka bani suna cewa mun dace
Dace ni nayi akan soyayya na more
Niko kawaye na da ganin ka suce mini sun kyasa
Ni sai nake cewa daga zuciya lallai sun kwafsa
Bani kara barin su sugan ka tun daga yau don kun gaisa
Sarewa nayi busa
Ajiyar ka in kai nesa
Yarda, sam babu akan kawaye karya ce
Dace ni nayi akan soyayya na more
Duk kyawo na budurwa in dai ba kece ba
Ban kallo da ido na sam bazan duba ba
Koda tayi kira na ni bazan amsa ba
Ban canza ba
Ke nayi duba
Bani in karba
Nayi maraba
Burina kullum kan soyayyar mu dake aure ce
Dace ni nayi akan soyayya na more
Junan mu da yarda, a tsakani babu fada a zaman mu na tare
Munyi fahimta, shiyasa bama da tunanin za muyi ware
Watarana kai ango niko in shiga sahu na amare
Naki na sare
Dole na jure
Mun rufe kyaure
In munyi aure
Bauta mun kama hanyar shaidan mun kauce
Dace ni nayi akan soyayya na more
Lokaci muke jira sai kazo
Inda rai rabon mu dole sai yazo
Babu kai kadai nake kira gwarzo
Inda kake ba kira kawai na zo
Zuciya na saki
Ba batun cire ki
Sa hannun ka dauki
Banyi maka tsaki
Babu shi babu duka a tsarin soyayya
Na sani babu duka a tsarin soyayya
Dace ni nayi akan soyayya na more
Dace ni nayi akan soyayya na more
Dace ni nayi akan soyayya na more
Written by: Umar M Shareef


