Letra

(Amude on the beat) Nayi shirin bin sahu na dau niyya Dan Allah mai sauraro kuma ga cikiya Zan zayano kamaninta don dubaiya Ka dauki alkalami zana in zaka iya In fado ma sufufin bazana kosa ba Karshen labarin da nake bamu hadu ba Kuma na dage neman ta nake bangaji ba Shekaru goma masoya na jira ba'a gaji ba Ayi hakuri masoya a'a badan ni ba Ku gyra zama labarin ban faro ba Tafiya ce nake tayi mai nisa Ban san ina zani ba ni na nausa Ga zuciya nata fadin karda in fasa Ina tafe nai karo da Dan Musa Yaso idan huta Ni ko nace, "Ban gaji ba" Allah ya kyauta haka zuciya take cewa Bari mana sai kun saba kafin shakuwa Abunda danaso da ki gane Ke kinyi mantuwa Tace akwai labarinta mai rikirtarwa Danaji labarin da tafiyar banyo ba Tafiya nake nisa nai karawa Na wuce Gombe Yanzu na shigo Adamawa An kira sallah Na dakata nayo tsayuwa Nauyin dake kaina sallah inyi saukewa Banjin dadin lokacinta yayo banyo ba Garin Fulani ne Adamawan Yola Nace amanar kyawu akai garin Yola Naga Lubabatu yar mutanen Yola Taji labarina har tana zubar kwalla Tace dani a soyayya banga komai ba A rayuwa lalai naga abun mamaki Iye a soyayya babban daki Nayi gamo a soyayya naiyo dauki Ni nai zaton soyayya da akwai zaki Na dandana sai naji akwai wani sirki Da dandano nima ban tantance ba Toh ko ke dai aljanace in ganki Mu hadu dake labari kibani in baki Tun randa na ganki nake son In sake kallonki Sai naji tashin muryar nan mai zaki Naji ance, "Juyo" Sai naji kamar bani ba
Writer(s): Hamidu Yusuf Halidu Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out