Letra

(Musax) (Musax beat) So, soyayya So, soyayya dakai na faro Oh-hh-hh-hh-hh Oh-hh-hh-hh So, soyayya dake na faro Ke nasaka a zuci bazan ciro ba Dukan damuwata na manta sanadinki Kina ban kulawarki ba kadan ba Ke kika ce dani so na zuci kin sawa Hakan ya sanya ni na daura danba Komai zanayo akan so sanadinki ne Ke kika nuna min kauna so a bayyane Kin zamto sarauniya a so ni bawanki ne Zan miki dukanin bauta komai na naki ne Kai, wayyo ni dadi Sanka a zuciya na daduwa Daren jiya nai bacci Kai nagani ka bani ruwa Ka zam min bango A zuciya kai ka sakan nutsuwa Da naji sautin muryar ka Na ganka nake kakuwa Matso gurina baby na In baka ruwa Auren mu shine burina A daura nai matsuwa Hubbi, hubbina Aurenki shine burina Nurul kalbina Nima dakai ne zan zauna Matso nan gefe na Zo ki zauna a dama na Gani a gefen ka Ban hanu inga furen kauna Kece dai wanda rai yake yiwa naci Bana so koda sakan naga kinyi takaici Burina aurenki diya ta mutunci Gaki da tarbiya ga kyau Kuma gaki da hanci Ga iya yin tafiya Kyan hali karda ka mance Har a gidan mu ance dani dake Ance mun dace Dakai na aminta kai kadai Zan ba zuciya ta Kai kazamto min madubi a rayuwata Kaine zaka bani kulawar ka Na kere mata Burina a daura aure Na zama maka mata Zan maka kwalliya ta burgewa Ba kazanta Ka zam min farin cikina Zauna ka huta So, soyayya So, soyayya dakai na faro (Mix) (Musax mix)
Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out