Похожие песни
Создатели
ИСПОЛНИТЕЛИ
Ali Jita
Исполнитель
МУЗЫКА И СЛОВА
Ali Jita
Автор песен
Слова
Ali Jita ne
Zakin waka
(Prince production)
So sinadari
Soyayya nada hadari
So ruwan zuma ne
Wani sa'in ruwan gubace kauna
So sinadari
Soyayya nada hadari
So ruwan zuma ne
Wani sa'in ruwan gubace kauna
So kala-kala ne
Mai nazari shi yakan yi lura
So sabida Naira
Koko so dan kyau na sura
Wani son a baki yake
A cikin zuciya da kura
Soyayya da mai hali
Irin halin hawainiya ne tsorona
So yana da dadi
Amma inda tatali da kauna
Mai sanka zuciya daya
Har abada bai saka ka rana
Mai yaudara butulci
Yaci amana ta so da kauna
Ka kyautata wa mai sonka
Inko kaki zakayo nadama wata rana
Jita ina kiran ku
Yan mata, samari yau mu duba
Mubar fishi da sauri
Mai hakuri shi yakan ci riba
Mu gane yanayin so
Sanyi ne da zafi sai mu saba
Ruwan ido a soyayya in har kayi
Kai karo da tarkon mummuna
Wata ran masoya
Aji dadi anata shewa
Wata ran a saba
Ayi kwana biyu ba hadewa
Kar mu dauki zafi
Dan Allah masoya muyi kulawa
Sai mu kauda zargin juna
Mai sa masoya suyo bankwana
So sinadari
Soyayya nada hadari
So ruwan zuma ne
Wani sa'in ruwan gubace kauna
So sinadari
Soyayya nada hadari
So ruwan zuma ce
Wani sa'in ruwan gubace kauna
(It's prince on the mix)
Writer(s): Ali Isa Jita
Lyrics powered by www.musixmatch.com