Music Video

Music Video

Credits

PERFORMING ARTISTS
Babangida Kakadawa
Babangida Kakadawa
Performer
COMPOSITION & LYRICS
Babangida Kakadawa
Babangida Kakadawa
Songwriter

Lyrics

Kai! gidan nan ba gida bane matsala dai ne gidan haya
Gidan nan ba gida bane matsala dai ne gidan haya
Duk wanda yake a gidan haya Allah ba shi wuri yayi nashi
Ko babu kudin buga kwano ya samu ko shifshi ya zuba sama
In kai haka ka hita kardagi tunda ka huta da biyan haya
Gidan nan ba gida bane matsala dai ne zaman haya
Kai gaka gidan haya
Wancen gashi gidan haya
Waccen gata gidan haya
Ku duka kun gamu kun hade
In kai kana da dangana kila wancen baya da dangana
Matsalar gidan haya
Ko da kun kai ku tara
Makewayinku guda ake
Matar wancen ta shiga
Matar wancen na jira
Kai kuma gaka kana jira
Shine matsalar zaman haya
In kana a gidan haya
Matarka bata da walwala
'Ya'yanta basu da walwala
Bakonka ba ya da walwala
In kay magana a kadammaka
Gidan nan ba gida bane
Matsala dai ne zaman haya
Babbar matsalar gidan haya
Yau! In an sanka tsakar gari
Gobe ana cimma gefen gari
Jibi ko kaje ka bidar wuri
Dan kana gudun ayi ma notice
Naji yan dako nata farin ciki
Yan baro nata farin ciki
Yan amalanke nata farin cikin
Wane zai tashi a gidan haya
Suna ta farin cikin sunyi sa'a da dakon curboard
Kai ka dace da bakin ciki
Gidan nan ba gida bane
Matsala dai ne zaman haya
Dan zaman haya mai ban tausay
Me ban taikaici dan zaman haya
Dan zaman haya me ban tausay
Shine wanda yana a gidan haya
Baya da harka wadda yake yi
Ga iyali kuma sun mai yawa
Mai ban takaici dan zaman haya
Karfi gaya da karfe gaya da harka wadda yakeyi
Amman ya rabe a gidan haya
Kuma yayi giji a cikin gidan
Wanga lalaci ne mai yawa
Kai tashi gidan nan ba na zama bane
Matsala dai ne zaman haya
Gidan nan ba gida bane
Matsala dai ne gidan haya
Akwai dan ragaitar zaman haya
Shine me mata hudu
Duk a gidan haya
Gidansu Bango yana gabas
Ga 'ya'yanta guda shida
Gidansu Gwamma yammaci
Ga 'ya'yanta guda shida
Gidansu Delu ina kudun
Ga 'ya'yanta guda shidda
Ga su Umma ya Turai nan kuma
Tare da Gwaggwan su duka
Ita ko ga goyo ga ciki
Wannan matsalar kaka take
Ku duka kun rufce a gidan haya
Malam ko noma zakayi se ka tanadi rumbu dan hatsi
Ya za kayi mata har hudu?
Kuma kowace na a gidan haya
Wanga lalaci ne mai yawa
Kai! Tashi gidan nan ba na zama bane
Tun farkon asalitan
Duk tsuntsun da yake sama
Ya gina gida nay ya shige
Kwarin da suke tudu
Kowane yayi gida ne ya shige
Hatta kwarin da suke ruwa
Ko wane yayi gida nai ya shige
Misali tun ga zanzaro
Gashi dai abu ne dan kankani
Yaje daji ya ja kasa ya debo ruwa nan ya hada
Ya gina gidan sa yana shiga
To kai matsayinka na dan Adam
Ya zaka tsaya a gidan haya
Kai! Tashi gidan nan ba na zama bane
Matsala dai ne gidan haya
Written by: Aminu Ladan Alan Waka
instagramSharePathic_arrow_out

Loading...