Music Video

Classic Hausa music, Gidan Haya
Watch {trackName} music video by {artistName}

Credits

PERFORMING ARTISTS
Aminu Ladan Alan Waka
Aminu Ladan Alan Waka
Performer
COMPOSITION & LYRICS
Aminu Ladan Alan Waka
Aminu Ladan Alan Waka
Composer

Lyrics

Kai, gidan nan ba gida bane Matsala dai ne gidan haya Gidan nan ba gida bane Matsala dai ne gidan haya Duk wanda yake a gidan haya Allah bashi wuri yayi nashi Ko babu kudin buga kwano ya samu ko sufti ya zuba sama In kayi haka ka fita kangi tunda ka huta da biyan haya Gidan nan ba gida bane Matsala dai ne zaman haya Kai gaka gidan haya Wancan gashi gidan haya Waccan gata gidan haya Ku duka kun gamu kun hade In kai kana da dangana kila wancan baya da dangana Matsalar gidan haya Koda kun kai ku tara Makewayar ku guda ake Matar wancan ta shiga Matar wancan na jira Kai kuma gaka kana jira shine matsalar zaman haya In kana a gidan haya, matar ka bata da walwala Ya'yan ta basu da walwala Bakon ka bayi da walwala In kayi magana a kadan maka Gidan nan ba gida bane Matsala dai ne zaman haya Babbar matsalan gidan haya Yau gobe an sanka tsakar gari Gobe ana cimma gafen gari Jibi ko ka jeka bidar wuri don kana gudun ayi ma notice Naji yan dako nata farin ciki Yan baro nata farin ciki Yan amalanke nata farin cikin wane zai tashi a gidan haya Suna ta farin cikin sunyi sa'a da dakon cupboard Kai ka dace da bakin ciki Gidan nan ba gida bane Matsala dai ne zaman haya Dan zaman haya mai ban tausayi Mai ban takaici dan zaman haya Dan zaman haya mai ban tausayi shine wanda yana a gidan haya Baya da harka wanda yake yi Ga iyali kuma sun mai yawa Mai ban takaicin dan zaman haya Gayi da karfi Gayi da karfe Gayi da aikin da yake yi ammah ya rabe a gidan haya Kuma yayi giji a cikin gidan Wanga lalaci ne mai yawa Kai tashi gidan bana zama bane Matsala dai ne zaman haya Gidan nan ba gida bane Matsala dai ne zaman haya Akwai dan ragaitar zaman haya Shine mai mata hudu duk a gidan haya Gidan su bango yana Gabas Ga ya'yan ta guda shida Gidan su Gwamma yammaci Ga ya'yan ta guda shida Gidan su Delu ina Kudun ga ya'yan ta guda shida Gasu umayya turai nan kuma tare da gogan su duka Ita ko ga goyo ga ciki wannan matsalar kaka take Ku duka kun rufce a gidan haya Malam ko noma za kayi sai ka tanadi rumbu don hatsi Ya za kayi mata har hudu kuma kowacce na a gidan haya Wanga lalaci ne mai yawa Kai tashi gidan nan bana zama bane Tun farkon asalatin duk tsuntsun da yake sama Ya gina gida nai ya shige Kwarin da suke tudu kowanne yayi gida nai ya shige Hata kwarin da suke ruwa kowanne yayi gida nai ya shige Misali tunda zanzaro gashi dai abine dan kankani Yaje daji yaja kasa ya debo ruwa nan ya hada Ya gina gidan sa yana shiga Toh kai matsayin ka na dan Adam ya zaka tsaya a gidan haya Kai tashi gidan bana zama bane Matsala dai ne gidan haya
Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out