album cover
Salsala
1,310
Country
Salsala was released on February 6, 2016 by Taskar Ala Global Limited as a part of the album Alfanda
album cover
AlbumAlfanda
Release DateFebruary 6, 2016
LabelTaskar Ala Global Limited
Melodicness
Acousticness
Valence
Danceability
Energy
BPM110

Credits

PERFORMING ARTISTS
Aminu Ala
Aminu Ala
Performer
COMPOSITION & LYRICS
Aminu Ladan Abubakar
Aminu Ladan Abubakar
Songwriter

Lyrics

[Verse 1]
Alfanda abin haka ne, mai dubu Gamji sha aune
Gamji jini na Annabi ne, da ga tsatso na fadima ne
Ba ku ji salsala ta sa ne, ta nasabar uba zane
Shehu jinin Usmanu ne, jika gurin dan Fodiyo ne
[Verse 2]
Fodiyo dan Muhammadu ne, Muhammadu dan Usmanu ne
Shi Usmanu dan Salihu ne, Salihu da ga Ayuba ne
Ayuba da ga Haruna ne, Haruna dan Masiranu ne
Masiranu Abdussamadu ne, shi kuma Abdussayyadu ne
[Verse 3]
Abdussayyadu Ilyasu ne, Ilyasu dan Akanbi'a ne
Akanbi'a Musa Jakolo ne, Jakolo da ga Yasi ne
Shi kuma Yasi dan Sunusi ne, Sunusi da ga Nizami ne
Nizami dan Alhassanu ne, Hassanu da ga Fadima ne
[Verse 4]
Fadima tsokar Annabi ne, Muhammadu shi afdalu ne
Cikamakin nubuwa ne, Gamji jini na Annabi ne
[Verse 5]
Alfanda mazan dauri Amadu Bello Sardauna
[Verse 6]
Alfanda mazan dauri Amadu Bello Sardauna
Alfanda mazan dauri Amadu Bello Sardauna
[Verse 7]
Kaliku kai na sa fari, ka karfafa mini sadari
Allah mujibu alkadiri, na yi riko da son Bashari
Alih sahabihi na gari, masu biyarka ba garari
Zan yi yabon mazan dauri Amadu Bello Sardauna
[Verse 8]
Alfanda mazan dauri Amadu Bello Sardauna
[Verse 9]
Amadu Gamji sha wake, ga ni tafe a dudduke
Masu yabo salon wake, sun fi dubu su ka yi wake
Alfanda gidan wake, Gamji maza icen marke
Ko a mafarki ko farke, ban ga kama da Sardauna
[Verse 10]
Alfanda mazan dauri Amadu Bello Sardauna
[Verse 11]
Ko a cikin dubun jama'a, Amadu yai daban zakka
Daga kama zuwa tsaiwa, Amadu yai daban zakka
Mai saje uban Inno, uban Luba ba ka da shakka
Dangarama icen rimi, ko daga nesa a gan ka
[Verse 12]
Alfanda mazan dauri Amadu Bello Sardauna
[Verse 13]
Gaba da baya kyan asali, gidan sarauta ga ilimi
Ga darajar gidan ilimi, ba inda bai aje kalami
Maliya mai hade kwatami, gata ga babba har karami
Kare da rago dukka guda suke ga Amadun ilimi
[Verse 14]
Alfanda mazan dauri Amadu Bello Sardauna
[Verse 15]
A tuna baya ba garari, Gamji farin uba na gari
Mai raba kaya ba fahari, kyauta kamar zubar madari
Mun sha zuma da ba hadari, mun gaza jure shan sukari
Gamji rashinka ne garari Amadu Bello Sardauna
[Verse 16]
Alfanda mazan dauri Amadu Bello Sardauna
[Verse 17]
Mai nada sarki cinye gari, mai cire sarki juya gari
Amadu yai abin fahari har gobe shi muke nazari
Dagi adon Arewa gari, Gamji mazan kwaran dauri
Rana mahaska dukka gari, Amadu Bello Sardauna
[Verse 18]
Alfanda mazan dauri Amadu Bello Sardauna
[Verse 19]
Ba shi da tsoro al asadu, shi aka tsoro mujtahidu
Amadu ya kai mujahidu yana cikin sahun shahidu
Ran juma'a shiri na kudu masu nifaka da makidu
Suka ishe shi Ahmadu. ya yi wafati Sardauna
[Verse 20]
Alfanda mazan dauri Amadu Bello Sardauna
[Verse 21]
Daga kisan su Amadu ne, har yau kasar take hautsine
Zubda jini su Amadu ne, don rikicin kabila ne
Mahassada suka yi aune, Arewa tai darin zane
Duk hikima ta Amadu ne, dangaramanmu Sardauna
[Verse 22]
Alfanda mazan dauri Amadu Bello Sardauna
[Verse 23]
Uba ga Inno Ahmadu ne, baba ga indo Ahmadu ne
Uban Lubaba Ahmadu ne jika ga Nana Ahmadu ne
Uban Muhammadu Amadu ne, ki gudu mai sa a gudu ne
Amadu dan Kabar tsaka ne, dama da hauni ba bone
[Verse 24]
Alfanda mazan dauri Amadu Bello Sardauna
[Verse 25]
Yeeh! Alhamdu godiya da yabo, Allahu sa in riski rabo
Daga yabo na masu yabo, 'yan asali da sun ci yabo
Ga gaisuwar Bukar Bako, wanda ya ce na tsara yabo
Gamji maza gaba ta rabo, sha yabo Gamji masu rabo
[Verse 26]
Alfanda mazan dauri Amadu Bello Sardauna
Alfanda mazan dauri Amadu Bello Sardauna
Alfanda mazan dauri Amadu Bello Sardauna
Written by: Aminu Ladan Abubakar
instagramSharePathic_arrow_out􀆄 copy􀐅􀋲

Loading...