Lyrics
Na damu dake kin damu dani 'kaunar mu tayo nisa
Ki ceci raina
Na baki kaina
Saboda kene zaya baya komai na
Ki yarda dani
Nasaki a ruhi na
Kin anshi kalami na, kin barni a rana dai
Kece kika sani na kamu da ciwon 'kauna
Na baki jiki zuciya harma ruhi na
Rana tsaka ga gashi kawai kin fara guduna
Me naimaki ki fadan ta sigar 'kauna
Nasan lamari hakanan yana sauyawa
Sannan harshe da hakori suna sabawa
Yawan afuwa 'kauna yake 'karawa
Zama na masoya zuciya sukeyin danna
Ko tsun-tsun so be ya tashi a kaina?
Kafin ya wuce afuwa muyiwa juna
Kinsan da hakora ne akeyin tauna
Da rana sani akace tanayin farga
Fata na gari zanai tayi ko yaushe
Irinta kikayi iyakar taimani kushe
Kinsanfa masoyinki nine nan 'karshe
Da ba mutuwa ba mai cireki a raina
Hannu na gari Allah yasa kiyi sauka
Ki kauda idonki a gajimaren kaka
Sannan doje baya da dadin tsinka
Idan da rabo zan 'kara saki idona
Daure ki fada man gunki ban saba ba
Shi tirbda masoyi kuskure ne babba
Sannan da rashin so bafa laifi ne babba
Hakkinki ina tsoron sakashi wuya na
Akwai wahala hakuri da sanki na manta
Sannan a idanuna kinada nagarta
Wani abu 'dai ya saka zama da kwadaita
Zamn aure to da na ida nufi na
Mai lasa zuma wataran zai kasa madaci
Zaman duniya bai hadani fada da makwabci
Mai yin hakuri shi zai zamo mawadaci
Allah Ahadun shine yasan zabi na
Hanta da jini ance min basu rabewa
Sabon yanayi kin daina bani kulawa
Da zan jure sai na kasa cin jarabawa
Naso mu kasance a cikin auren mu na sunna
Na samu canji tindaga lokacin da kukai kwalli
Da kwarkwasa 'dakina ta 'kera muhalli
Sanin asali shikesa kare yaci alli
Riba ga masoya akace ruko da amana
Abinda kike so zanso dai-dai kika zaba
Fatan da nake gun zabinki karda kiyi kwaba
Domin wahala ce kesa maciji saba
Mai ciwon so bashida magani sai 'kauna
Dadin baki shine ke kawar da tunani
Asalin hali baya bayyana a kamanni
Kayan guzuri na mai tafiya hutu da mazauni
Duk wanda yasan darajar tanda zai girmama waina
Gareki nazam mai uzuri na gane nufinki
Abinda akai hita ne in babu saninki
Domin kwa dukan sirri nawa bani rufan ki
'kaunarki nasa ta ratsan dukan tsarina
Ranar rabuwa tilas ne azubda hawaye
Wajen 'ya 'ya wajib ne biya ga iyaye
Kar ki biyewa sharrin zuciya da 'kawaye
Nima 'da ne in na shige cikin dangina
Dadi wahala in muka samu kai Allah ne
Shi munka sani wanda yake tayar da na zaune
'kaunarki ina 'kara fadin ke taiwa zane
Na gane nufinki kema kyau ki gane nufina
In banda sila sai ince mudinga zumunta
Domin a sufar 'kauna naga babu mugunta
Wadanda sukayo maki zabin yau sun 'bata zumunta
Nayi maku fatan kairi a tare ku zauna
Lyrics powered by www.musixmatch.com